Bidiyo: Na kashe mutane fiye da 50, na samu kudi kusan miliyan N700 - Mai garkuwa da mutane

Bidiyo: Na kashe mutane fiye da 50, na samu kudi kusan miliyan N700 - Mai garkuwa da mutane

Wani mai garkuwa da mutane da wakilin sashen gurbataccen yaren turanci (Pidgin) na kafar watsa labarai ta kasar Birtaniya (BBC) ya gana da shi ya bayyana yadda ya kashe mutane fiye da 50 tare da samun kudi kusan miliyan N700 a cikin shekara daya.

Ya bayyana cewa su na kiran fita farautar mutane 'su' (kamun kifi) cikin yaren Turanci (Fishing). Ya kara da cewa basa sa ran za su dawo gida da rai duk lokacin da suka fita satar mutumin da za su yi garkuwa da shi.

Kazalika, ya bayyana cewa harkar satar mutane tare da yin garkuwa da su na da matukar hatsari, saboda harka ce ta 'ko a mutu ko a yi rai'.

Mai garkuwa da mutanen ya ce bai yi nadamar abinda ya aikata ba, tare da bayyana cewa ba ya daukan wani mataki sai ya tabbatar da cewa zai amfane shi.

Kalli faifan bidyon hirar da aka yi da shi a kasa.

Ko a kwanakin baya saida Legit.ng ta kawo labari mai alaka da wannan inda jaridar Vanguard ta ziyarci wata magarkama da babban sifeton 'yan sanda na kasa (IGP) ya sa aka ware domin ajiye masu garkuwa da mutane da aka kamo daga sassan kasar nan.

A ganawar da wakilin jardar ya yi da masu garkuwa da mutanen, wani daga cikinsu mai shekaru 45 a duniya ya bayyana cewar yana da mata uku da yara 11 wadanda yake daukar nauyi daga muguwar sana'ar da ya ke yi.

Mutumin mai suna Sani Ibrahim, wanda aka fi sani da Kwalba saboda shan giya, ya bayyana cewar garkuwa da mutane ta yi masa rana domin ya samu kudi fiye da wadanda ya samu lokacin da ya fara sata kafin daga bisani ya koma fashi da satar shanu.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Kotu ta yi watsi da wata bukatar Atiku da PDP a kan zaben Buhari

A cewarsa, aikin ta'addanci ya biya shi saboda da irin kudin da ya samu daga aikata laifuka ne ya auri mata uku da suka haifa masa yara 11. Sannan ya kara da cewa koda yaushe yana cikin kudi, lamarin da ya sa giya da mata basa yanke masa.

Da yake bayar da labarin yadda ya zama mai garkuwa da mutane, Ibrahim ya bayyana cewa: "na fara garkuwa da mutane ne a kan wani mutum da ya samu sabani da yaro na. Mun yaudare shi tare da tsare shi a tare da mu har sai da mutanensa suka kawo mana N400,000 kafin mu sake shi."

Daga wannan lokaci ne idon Ibrahim ya bude da garkuwa da mutane har ta kai ga ya bar sauran aiyukan ta'addanci da ya ke aikata wa tare da koma wa yin garkuwa da mutane kawai.

Kazalika ya bayyana cewa daga nan ne ya shiga harkar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa har zuwa lokacin da ya hadu da Buharin daji, wani gawurtaccen dan bindiga da aka kashe a jihar Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel