Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya
Bisa ga dukkan alamu liyafa na cigaba da bunkasa ga fitattacen jarumin Kannywood, Adam A Zango.
A kwana-kwanan nan ne jarumin ya dauki hoto tare da sabuwar motar da ya siya ta alfarma mai suna Wrangler Jeep wacce aka kiyasta kudin ta ya kai naira miliyan 23 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A yayin da ya ke nuna hotunan sabuwar motar a shafinsa ta sada zumunta na Instagram a ranar Talata, jarumin da ake yi wa lakabi da Prince Zango ya yi alfahari cewa wannan lokaci ne da banbanta kansa daga sauran jurumai.
DUBA WANNAN: Kungiyar goyon bayan matasa a siyasa ta yi alla-wadai da Sanata Elisha Abbo da ya mari wata mace
Jarumin ya mika goditarsa ga Allah bisa ikon da ya bashi na mallakar sabuwar motar.
Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa farashin 2019 Wrangler Jeep a kasuwanni ya kai fam 49, 990.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng