Babbar magana: Ina goyon bayan a bawa 'yan luwadi da madigo 'yancin yin auren jinsi - Amina Mohammed

Babbar magana: Ina goyon bayan a bawa 'yan luwadi da madigo 'yancin yin auren jinsi - Amina Mohammed

- Ranar Asabar dinnan da ta gabata ne Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar dinkin duniya ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter

- Amina Mohammed ta wallafa cewa tana goyon bayan samar da daidaito tsakanin 'yan luwadi da 'yan madigo a duniya

- Wannan magana da Amina tayi ta jawo kace-nace sosai a shafukan sada zumunta, inda mutane da yawa suke Allah wadai da wannan furuci nata

Jiya Litinin ne 1 ga watan Yuli, 2019 jaridar The Cable ta ruwaito cewa, tsohuwar ministar Buhari wacce ta zama Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta wallafa wani rubutu a shafinta na Twitter ranar Asabar din da ta gabata, inda tayi kira da a baiwa 'yan luwadi da madigo damar yin auren jinsi.

Wannan abu da Amina ta wallafa, ya janyo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta, inda mutane da yawa suke Allah wadai da wannan abu da ta fada.

KU KARANTA: Babbar magana: Daga yin wasa da lamarin aure Zainab da Sunusi sun angwance a shafin Facebook

Inda wasu suke ganin cewa bata yiwa addininta, kasarta, al'ada, da yarenta adalci ba, indan har za ta yi kira akan a daidaita tsakanin 'yan luwadi da madigo, hakan yana nufin ta ajiye addini, al'ada da duk wata tarbiyya data taso da ita a kasar Hausa.

To sai dai wasu suna ganin hakan da tayi ba komai bane, tunda dama matsayin da aka bata a majalisar, matsayine da yake bukatar hakan, saboda haka dan tayi kira akan a samu daidaiton mu'amala tsakanin masu luwadi da madigo, ba abin mamaki bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel