Karan kwana: Uwargida ta jibga ma Mijinta icce, ya sheka barzahu
Wata mata mai suna Bilkisu Isah ta jibgi mijinta, uban yayanta da wani makeken icce a gidansu dake unguwar Sabon Tahsa cikin garin Abaji na babban birnin tarayya Abuja, inda nan take ya fadi matacce.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani makwabcin ma’auratan mai suna Salihu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis data gabata da misalin karfe 9:12 na dare sakamakon sa-in-sa data kaure tsakanin ma’auratan.
KU KARANTA; Gwamna Ganduje yayi nadin sabbin mukamai masu muhimmanci guda 26
A cewar Salihu, Mijin matar mai suna Isah Egba ya rufe Bilkisu da fada ne akan fita da tayi daga gidansu ta bar yayansu 5 suna gararamba, kuma ba tare da neman izininsa ba, har sai karfe 8 na dare ta dawo, daga nan sai ya umarceta daga fitan masa daga gida.
Malam Isah bai tsaya nan ba sai ya rarumi uwargida Bilkisu da nufin fitar da ita da kansa daga gidan, hakan ne ya bata ma Bilkisu rai, inda ta rarumi wani katon icce ta maka masa a kai, nan take ya yanke jiki ya fadi, jini na ta kwarara daga kansa.
Makwabtansu ne suka yi kokarin garzayawa dashi zuwa Asibitin Abaji cikin gaggawa, inda daga nan aka mikashi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja, amma bai yi tsawon rai ba, inda ya cika a cikin daren.
Da majiyar Legit.ng ta tuntubi rundunar Yansandan Abuja don jin ta bakinsu, sai kaakakinta, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar mata da aukuwar lamarin, kuma yace sun kaddamar da bincike akan lamarin, amma a yanzu suna farautar uwargida Bilkisu bayan ta ranta ana kare.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng