Rikicin Ganduje da Sanusi: Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi karin mutane su shiga cikin lamarin

Rikicin Ganduje da Sanusi: Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi karin mutane su shiga cikin lamarin

Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su sanya baki a lamarin rashin jituwan da ke tsakanin Sarkin Kano, Mohammad Sanusi II da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ya bayyana kiran ne jiya Lahadi, 30 ga watan Yuni a wata hira da manema labarai a gidansa da ke Bauchi.

Yace: “Abun da ya faru a Kano tsakanin masarautar jihar da gwamnatin jihar ya kasance abun bakin ciki. Nayi magana ne a lokacin da rikicin yayi tsauri kuma na bayyana cewa Kano ya kasance yanki mai muhimmanci a Najeriya. Kusan kowa a Najeriya, musamman mu da muka fito daga yankin arewa, muna da muhimmanci a Kano.

“Haka zalika, Kano tana da muhimmanci kuma ta wuci ace tana cikin rikici musamman ma wanda ya hada da masarautarta na kwarai, al’adun gargajiya ko makamancin haka.

“Mu sani cewa ofisoshin siyasa suna mulki shekaru hudu ko takwas ne. Suna zuwa suna kuma wucewa kamar yanda cibiyoyin al’adun gargajiya da mutane ke shafewa.

KU KARANTA KUMA: Ya kama ta dukkanin yan Najeriya su kasance da yanci guda a jihar da suke da zama – Sarki Sanusi

“Ya cancanci Gwamnan ya ba masarautar girmanta kuma dole masarautar ma ya ba da girma ga gwamnati. Dole a girmama masarautan saboda tana bayar da umurnin ga mutane kuma siyasa ba zai yiwu ba idan ba tare da goyon bayan mutane ba yayin da, a bangarenta, dole masarautar ta fahimci cewa lokuta sun canja, gwamnatin na da alhakin nada sarakuna”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel