Abba Kyari: Wasu Jakadan Najeriya su na cigaba da aiki duk da zarce shekarun aiki

Abba Kyari: Wasu Jakadan Najeriya su na cigaba da aiki duk da zarce shekarun aiki

Sahara Reporters ta kawo rahoto cewa wasu Jakadun Najeriya da su ka zarce shekarun ritaya su na cigaba da aiki tarna e da karbar alawus da kudin aiki na miliyoyin daloli wanda ya sabawa dokar aiki.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, Malam Abba Kyari, shi ne ya yi watsi da umarnin shugaba Buhari na dakatar da Jakadun daga aiki.

Jaridar ta ce akwai akalla Jakadu 25 na Najeriya da ya kamata a ce sun yi ritaya tun a tsakiyar shekarar 2018, sai dai har yanzu sun yi kememe sun cigaba da zama a ofis su na karbar albashi da alawus.

Daga cikin Jakadun kasashen da ya kamata a ce sun dawo gida akwai Jakadun Morocco, Kamaru, Kuba, Austriya, Kenya, Beljika, Mali, Indonesiya, Filifins, Sanagal, Hungary, da na Jamhuriyyar Czech.

KU KARANTA: Zaben 2019 ya jawo rigimar da ake yi a cikin fadar Shugaban kasa - PDP

Akwai Jakadun Najeriya masu uwa a gidin-murhu da su ke rike da mukaman na su duk da sun isa shekaru 60 a Duniya ko kuma sun yi akalla shekaru 35 su na aiki a dalilin kusanci da Malam Abba Kyari.

A Disamban 2018, Ministan harkokin wajen Najeriya a lokacin, Geoffrey Onyeama, ya gana da shugaban kasa Buhari a game da yi wa Jakadun kasar ritaya, kuma ya samu amincewar shugaban kasar.

Daga baya Ministan ya aika takarda a madadin shugaban kasa Buhari ga wadannan Jakadu su ajiye aiki. Daga baya babban Hadimin shugaban kasa, Abba Kyari ya kyale wadannan Jakadu na-kusa shi a ofis.

Rahotannin sun nuna cewa babban dalilin da ya sa a ka bar wadannan Jakadu da wasu sababbi da aka nada a bakin aiki shi ne kusancin su da COS Abba Kyari da kuma shugaban NIA na kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel