Kungiyar Manchester United ta ambaci farashin da za ta sayar da Pogba

Kungiyar Manchester United ta ambaci farashin da za ta sayar da Pogba

Wata jaridar harkokin wasanni, 'The Mirror' ta wallafa rahoton cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester Unite ta tsayar da kudin kasar Ingila Yuro miliyan 150 a matsayin farashin dan wasanta, Paul Pogba.

Idon kungiyoyin Realmadrid da ke kasar Andolus (Spain) da Juventus da ke kasar Italiya na kan Pogba, dan wasan tsakiya na kungiyar Mancester United.

Pogba na son barin kungiyar Manchester United bayan ya bayyana cewar lokaci ya yi da ya kamata da ya kamata ya kara gaba bayan an fitar da kungiyar Manchester daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Sai dai ana ganin cewa Manchester United ta saka farashin da zai yi wuya ya bar Pogba ya bar kungiyar.

Manchester United ce ta raini Pogba tun yana karami amma daga baya ta sayar da shi ga kungiyar Juventus.

DUBA WANNAN: Ba na yaudarar 'yammata - Mai kama da Messi 'kamar an tsaga kara'

Bayan Pogba ya samu shahara a kungiyar Juventus ne sai kungiyar Manchester United ta koma zawarcinsa, har ta kai ga ya dawo taka mata leda.

Ita kan ta yanzu kungiyar Juventus, ta dawo zawarcin Pogba da karfinta, sai dai ta na fuskantar kalubale daga kungiyar Real Madrid.

Masu hasashen kwallon kafa na ganin cewa ra'ayin Pogba ya fi karkata a kan koma wa kungiyar Realmadrid domin yin aiki da mai horar wa, Zinedine Zidane, wanda suka fito daga kasa daya tare, wato kasar Faransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng