Ba na yaudarar 'yan mata - Mai kama da Messi

Ba na yaudarar 'yan mata - Mai kama da Messi

- Reza Paratesh, dan asalin kasar Iran, ya shiga tsaka mai wuya, bayan an zarge shi da yaudarar 'yammata ta hanyar nuna musu cewa shine Messi na gaskiya

- Idan aka tabbatar da zargin da ake yi masa, za gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhumarsa da aikata fyade ta hanyar yaudara

- Sai dai Paratesh ya musanta zargin da ake yi masa tare da yin barazanar garzaya kotu domin neman hakkinsa, bisa bata masa suna da aka yi

Reza Paratesh, mutumin nan mai tsananin kama da fitaccen dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya musanta rahoton da ya bayyana cewa ya yaudari wasu 'yammata wajen yin lalata da su, ta hanyar yin sojan gonar cewa shi ne Messi na kasar Argentina.

Paratesh na tsananin kama da Messi, lamarin da yasa ake zargin cewa yana yaudar jama'a, musamman 'yammata, ta hanyar nuna musu cewa shine Messi na ainihi da suke ji da gani a akwatunan talabijin dinsu.

DUBA WANNAN: AGF ya fitar da alkaluman kudin da FG ta raba wa jihohi da kananan hukumomin a watan Mayu

A cikin makon da muka yi bankwana da shi ne wata jarida wasanni mai suna MARCA da ke kasar Andolus (Spain) ta wallafa rahoton cewa Paratesh na nuna cewa kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, saboda tsananin kama da Messi, domin 'yammata su saki jiki da shi.

Matukae aka tabbatar da wannan zargi, za a tuhumi Paratesh da laifin aikata fyade ta hanyar yaudara.

Sai dai Paratesh, wanda ake kira Messin kasar Iran, ya musanta wannan zargi a shafinsa na 'Instagram' tare da yin barazanar garzaya wa kotu domin domin neman hakkinsa, bisa abin da ya kira bata masa suna da aka yi.

Tun bayan da aka gano kamar da ya yi da Messi ake zarginsa da yin sojan gona, zargin da Paratesh ya sha musanta wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel