Kabusu: Ina shan karan sigari 60 a kowacce rana - Sabon kocin Juventus
Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Maurizio Sarri, wanda yanzu ya koma kungiyar Juventus, ya bayyana cewar ya na shan karan sigari 60 a kowacce rana.
Sarri, mai shekaru 60 a duniya, tsohon ma'aikacin banki ne da ke da kwarewa a harkar kwallon kafa da zukar tabar sigari.
Ya na shan a kalla kwalin sigari hudu a kowacce rana, lamarin da ya ce ya na nema ya wuce gona da iri.
"Ina san karan sigari 60 a kowacce rana, wanda ko a wurina hakan ya yi yawa," Sarri ya shaida wa La Nuova Riviera, wata kafar watsa labaran wasanni a kasar Italiya.
An yi kiyasin cewa Sarri na kashe kudin kasar Ingila Yuro 1,400 a sayen taba sigari kowanne wata.
"Ba na shan sigari yayin da ake buga wasa, amma da zarar an tashi ya zame min dole na zuki sigari.
"Ina fama da matsanancin ciwon baya a 'yan kwanakin baya bayan nan, amma yanzu ina samun sauki," a cewar Sarri.
Sarri ya samu nasarar lashe kofin gasar nahiyar Turai (UEFA EUROFA CUP) na kakar wasan bana a kungiyar Chelsea. Sai dai hakan bai sa kungiyar ta cigaba da aiki tare da shi ba saboda ya gaza taka rawar gani a gasar cin kofin kungiyoyin kwallon kafa na kasar Ingila.
DUBA WANNAN: Toshon ministan tsaro a Najeriya ya sayi Otal din kasar Ingila mai shekaru 300 a kan biliyan N1
Kafin zuwansa Chelsea a bara, Sarri ya kasance kociyan kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italy.
Yanzu haka Sarri ya rattaba hannu a kwangilar aiki da kungiyar Juventus da ke kasar Italy na tsawon shekaru uku.
Da yake magana a kan komawarsa kungiyar Juventus da aiki, Sarri ya ce: "na kan tashi da daddare domin yin tunanin yadda zan samu nasara a kan kungiyar Juventus a tsawon shekaru uku da na yi ina aiki a Napoli amma duk da haka ba na iya samun nasara a kan su. Yanzu ga shi ita ce kungiyar da zan yi wa aiki hanta da jini domin ta samu nasara."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng