Yanzu-yanzu: Wani katafaren bene mai hawa uku da ake gina wa a Legas ya rushe
Wani katafaren bene mai hawa uku da ake gina wa a yankin Iju a jihar Legas ya rushe a daren ranar Laraba.
Ginin, wanda ake kan da aikinsa, ya ruso a kan jama'a da dama.
Da yake tabbatar da rushewar ginin ga manema labarai, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, sabon shugaban hukumar bayar da agajin gagga wa ta jihar Legas (LASEMA) ya ce: "ina mai sanar da ku cewa wani ginin bene mai hawa uku ya rushe a unguwar Fagba da ke kan hanyar zuwa Ijju.
"Ginin, wanda ake kan aikinsa, ya ruso a kan jama'ar da ke cikinsa. Ba a samu asarar rai ba sakamakon rushewar ginin, kuma an garzaya da jama'ar da aka ceto zuwa asibiti domin duba lafiyarsu
"Dukkan jami'an mu da masu ruwa da tsaki a bangaren bayar da agaji a jihar Legas na wurin da ginin ya rushe domin bayar da gudunmawarsu.
DUBA WANNAN: Kazanta da rashin kunya: Kotu ta rushe auren Baraka da Ibrahim
"Za a karasa rushe ginin tare da baje wurin da ake gina benen domin kare jama'a da ke zaune a yankin.
"Za mu gudanar da gwaje-gwaje a gidajen da ke makwabataka da ginin domin tabbatar da ingancin lafiyarsu," a cewar sa.
Rushewar ginin na zuwa ne cikin 'yan kwanaki kalilan bayan wani ginin ya rushe a yankin unguwar Oshodi da ke jihar Legas.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng