Labari mai dadi: Hukumar 'yan sanda za ta fara tantance mutane 210,150 da za ta dauka aiki ranar 1 ga watan Yuli

Labari mai dadi: Hukumar 'yan sanda za ta fara tantance mutane 210,150 da za ta dauka aiki ranar 1 ga watan Yuli

- Hukumar 'yan sanda ta kasa ta bada sanarwar za ta fara tantance mutane 210,150 da ta fitar da sunayensu domin daukar aiki

- Hukumar ta ce za ta fara tantancewar ne ranar 1 ga watan Yuli inda za ta kammala ranar 28 ga watan Yuli

- Ta kuma bayyana cewa ta aikawa duka mutanen da abin ya shafa sako ta adireshin su na yanar gizo, da sakon yadda abubuwa za su wakana

Hukumar 'yan sanda ta kasa ta ce ranar 1 ga watan Yuli za ta fara tantance mutane 210,150 da ta fitar wadanda za ta dauka aiki.

Hukumar ta ce fara tantance mutanen a ranar 1 ga watan Yuli zuwa ranar 28 ga watan Yuli, a dukkanin jihohi 36 na fadin kasar, ciki hadda babban birnin tarayya Abuja.

Ranar 11 ga watan Janairu da hukumar ta rufe shafinta na karbar ma'aikatan, hukumar ta bayyana cewa mutane 315,032 ne suka cika aikin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne dai ya bawa hukumar 'yan sandan umarnin daukar ma'aikata mutum dubu goma.

KU KARANTA: Tirkashi: Wasu barayi sun afka gidan alkali, sun sace gwala-gwalai na miliyan 30

A cikin mutanen da hukumar ta saki sunayensu, 182,926 maza ne yayin da aka samu mata 27,224.

A wata sanarwa da hukumar ta yi jiya Laraba a Abuja, ta bakin kakakin ta na kasa, Ikechukwu Ani, ya bayyana cewa an tura wa duka mutanen da abin ya shafa sako ta adireshin email din su, wanda yake dauke da wuri, rana, lokaci da kuma dukkanin abubuwan da ake bukata ranar tantancewar.

Ani ya kara da cewa duka mutanen za su duba sunayensu a shafin hukumar 'yan sanda mai adireshi kamar haka www.psc.org.ng

A karshe ya shawarci mutanen da kada suyi ha'inci ko kuma su baiwa ma'aikatan hukumar cin hanci, inda ya kara da cewa idan aka kama mutum da irin wannan laifin za a kama shi.

Sannan ya shawarci ma'aikatan hukumar da suyi aiki tsakani da Allah wurin tantance mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel