Malabu: Tsohon Jakadan Rasha, Ednan Agaev, ya bayyana a gaban kotun Italiya

Malabu: Tsohon Jakadan Rasha, Ednan Agaev, ya bayyana a gaban kotun Italiya

Wani babban jami’in kasar Rasha, Ednan Agaev, ya hallara gaban babban kotun da a ke shari’a a kan wani rijiyar man Najeriya da a ka saida a lokacin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kamar yadda Premium Times ta rahoto a Ranar 26 ga Watan Yuni, 2019, Ednan Agaev ya halarci zaman kotun da a ka yin a Ranar Larabar nan. Ana wannan shari’a ne a Birnin Milan na Italiya.

Agaev babban Dillali ne a kasar Rasha wanda da shi a ka yi cinikin rijiyar mai na OPL 245 tsakanin gwamnatin Najeriya da kuma kamfanonin Shell da kuma Eni a cikin shekarun baya.

Fitaccen dillalin ya taba bayyana cewa wani tsohon Ministan mai na Najeriya, Dan Etete, ya nuna masa niyyarsa na karbar toshin baki na akalla Dala miliyan 400 idan su ka kare cinikin rijiyar man.

KU KARANTA: 2019: Kotu ta dage sauraron karar Atiku sai watan gobe

Wannan Bature ya na ganin cewa idan har a ka ba Dan Etete Dala miliyan 400 a matsayin cin hanci, akalla shugaban kasa Goodluck Jonathan zai tashi da Dala miliyan 200 daga cikin kudin.

Mista Agaev ya na cikin wadanda a ke tuhuma da laifin badakala wajen cinikin wannan rijiya na Najeriya. Yanzu haka, kamfanonin da a ke shari’a da su, sun ki ba kotu shaidar da a ke bukata.

A shekarar 2018 ne kasar Rasha ta nemi kotun da ke wannan bincike da ta dakatar da shari’ar. A na wannan shari’a ne a babban birnin kasar Italiya. Agaev dai tsohon Jakada ne na kasar Rasha.

Jaridar ta ce an ga Mista Agaev a cikin kotu a Ranar Laraba da safe inda zai cigaba da amsa zargin da a ke yi masa. Kawo yanzu dai babu wani labari a game da yadda shari’a ta kasance.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel