Kano: Nazir Sarkin waka ya yiwa Gwamna Ganduje wani habaici a sabuwar wakar da ya fitar
- Shahararren mawakin Hausan nan, Nazir Ahmad Sarkin Waka, ya yiwa gwamnan Kano wani habaici a sabuwar wakar shi
- Mawakin ya yabi Sarkin Kano Muhammadu sanusi II, inda kuma ya juya harshe ya yiwa gwamnan jihar wani habaici a cikin kalamansa
- Wannan dai shine karon farko da makawakin yayi magana dan gane da raba masarautun jihar da aka yi zuwa gida biyar
Shahararren mawakin Hausan nan, Nazir M Ahmad, Sarkin Waka, yayi wani habaici da wasu kalamai na waka da suka yi nuni da cewa da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ke.
Wannan shine karon farko da Naziru yayi magana akan lamarin rikicin masarautar jihar, tun bayan da gwamnatin jihar ta raba masarautar zuwa gida biyar.
A kalaman da Nazirun yayi ya nuna goyon bayansa ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, inda kuma ya yiwa gwamnan jihar habaici a cikin kalamansa.
KU KARANTA: Zamfara: Ban bar bashin ko kwabo ba a Zamfara - Tsohon gwamna Abdulaziz Yari
Wakar wacce ya sanyawa suna "Mata ai kidan Tabare"
Ya ce: "Shekaru dubu ana tare. Ke kaza kinzo da tone-tone, kin tona rami har hudu dan garaje."
"Sarki mai martaba, iko na Allah wannan ta tabbata, mai ja da ikon Allah dan wahala ne, mai shawara aikin shi bashi baci, makaryaci kullum dan yaudara ne, mu bauta Allah shine wanga zance, mai bin iyaye wannan riki dace."
"In sun so Sanusi sarkin su, in ma ba sa so Sanusi sarkin su."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng