An kama 'yan leken asirin masu garkuwa da mutane 3 da wasu bata gari 32 a Kebbi

An kama 'yan leken asirin masu garkuwa da mutane 3 da wasu bata gari 32 a Kebbi

Rundunar 'Yan sanda reshen Jihar Kebbi ta ce ta kama wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane 10 da 'yan leken asiri uku da kuma wasu bata gari 32 karkashin atisayen 'Operation Puff Adder' da Sufeta Janar na 'Yan sanda Muhammadu Adamu ya gabatar domin magance laifuka a sassan kasar nan.

Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Garba Danjuma ne ya bayar da sanarwar yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi babban birnin jihar a ranar Wednesday.

Ya ce dabarun rundunar ne ya yi sanadin kama wadanda ake zargi da aikata laifukan tsakanin watan Mayu zuwa Yunin wannan shekarar.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun tashi kauyen Rafin Kada, sun kashe mutane da dama

"Munyi nasarar kama 'yan leken asirin masu garkuwa da mutane uku da masu garkuwa da mutane 10 da kuma wasu bata gari 32 tare da makamai daban-daban, wayoyin salula da komfuta da wukake da adduna a karkashin atisayen Operation Puff Adder.

"An kama wadanda ake zargi da yi wa masu garkuwa da mutanen leken asiri ne a ofisoshin 'yan sanda daban-daban a karamar hukumar Danko Wasagu na jihar.

"Sun kware wurin ba wa masu garkuwa da mutane bayyanan sirri musamman wadanda ke sace mutane a Zamfara da Kebbi da garin Bena da ke yankin Danko/Wasagu," inji shi.

Mista Danjuma ya ce sauran wadanda aka kama ana zarginsu da aikata muggan ayyuka ne kamar fashi da makami, satar babur, fyade da mallakar miyagun makamai da sauransu.

"Da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu," inji shi.

Kwamishinan ya shawarci al'umma su cigaba da sanya idanu kan abubuwan da ke faruwa a unguwaninsu tare da sanar da 'yan sanda saboda inganta tsaro a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel