Babbar magana: Nan da shekara 27 mutane za su daina mutuwa, kuma za a samo maganin tsufa - Masana

Babbar magana: Nan da shekara 27 mutane za su daina mutuwa, kuma za a samo maganin tsufa - Masana

- Wasu masana sun bayyana wasu dalilai masu karfi akan wani muhimmin bincike da suka yi

- Masanan sun bayyana cewa nan da shekara 27 mutane za su daina mutuwa, sannan kuma za a samo maganin da zai ke warkar da tsufa

- Sannan masanan sun bayyana cewa nan da shekaru 10 za a gama bincike akan maganin cutar daji

Nan da shekaru 27 kawai, mutane sai sun ga dama za su mutu, sannan za a samar da maganin da zai ke warkar da tsufa, a cewar wasu kwararru guda biyu na bangaren kimiyya, a lokacin da suke gabatar da wani littafi da suka rubuta a birnin Barcelona na kasar Spain.

Jose Luis Cordeiro, an haifeshi a kasar Venezuela, da kuma kwararre a fannin lissafi, kuma wanda ya samar da manhajar kwamfuta ta 'Symbian, David Wood, sune suka gabatar da littafin, inda suka bayyana cewa da gaske ne za a zo lokacin da sai mutum ya ga dama zai mutu.

Mutane kawai za su dinga mutuwa ne ta bangaren hatsari, ko kuma rashin lafiya, a nan da shekara 27, in ji Cordeiro da Wood, sannan sun bayyana cewa tsufa ma an fara ganin shi a matsayin rashin lafiya, saboda haka za a maida kai wurin nemo maganinsa.

Za su samo maganin tsufan ne ta hanyar, juyar da tsofaffin kwayoyin cutar tsufan na jikin dan adam su zama sabbi, sannan a cire kwayoyin cutar da suka mutu a jikin mutum, hakan shine zai kawo karshen tsufan da mutane keyi.

Cordeiro, wanda yake a Jami'ar Fasaha ta Massachusetts wato Massachusetts Institute of Technology (MIT) dake kasar Amurka, ya ce ya zabi cewa ba zai mutu ba, kuma nan da shekara 30 zai samo maganin da zai cire tsufan dake jikin shi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Masana'antar Kannywood na dab da daina aiki har abada - Zaharaddeen Sani

Bayan haka kuma Cordeiro da Wood sun yarda cewa nan da shekaru 10, za a samo ingantaccen ciwon daji, kuma manyan kamfanoni na fasaha irinsu Google za su shiga bangaren lafiya, saboda sun fara gano cewa akwai maganin tsufa.

Kamfanin Microsoft ya riga ya sanar da cewa ya bude cibiya da masana fannin kimiyya za su gabatar da bincike game da maganin cutar daji, kuma nan ba da dadewa ba za a gano maganin.

Masanan sun bayyana cewa duk da dai mutane ba su da masaniya akan binciken, amma an gano binciken a shekarar 1951, inda aka gano cewa kwayar cutar daji ba ta mutuwa, bayan an cire kwayar cutar a jikin Henrietta Lacks wacce ta mutu sanadiyyar cutar, amma har ya zuwa yanzu kwayar cutar na nan da ranta.

Rashin mutuwa ba wai yana nufin cewa duniyar za ta cika ba, masanan suka ce: "Akwai wuri isasshe da mutane za su zauna a duniya, kuma a wannan lokacin mutane ba sa haihuwa kamar yadda ake haihuwa a da, sannan kuma akwai yiwuwar zuwa lokacin mutane sun fara zama a sararin samaniya.

"Kasar Japan da Koriya, idan har suka cigaba da al'adar su ta kin haihuwa, akwai yiwuwar nan da karni biyu za su kare a doron duniya," in ji Cordeiro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel