Wata sabuwa: Masana'antar Kannywood na dab da daina aiki har abada - Zaharaddeen Sani

Wata sabuwa: Masana'antar Kannywood na dab da daina aiki har abada - Zaharaddeen Sani

- Daya daga cikin manyan jaruman wasan fina-finan Hausa na Kannywood yayi wani muhimmin kira ga gwamnatin Najeriya

- Inda ya bukaci gwamnati ta kai masana'antar tasu dauki domin farfadoda masana'antar wacce ke shirin lalacewa

- Jarumin ya ce masana'antar ta kama hanyar lalacewa, kuma taimakon gwamnati ne kawai zai iya ceto ta

Fitaccen jarumin wasan fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood Zaharadden Sani ya bayyana cewa masana'antar Kannywood ta kama hanyar lalacewa, kuma taimakon gwamnatin kasar nan ne kawai zai ceto ta daga halin da take ciki.

"Yanzu babu riba ko kadan a harkar fim, asara kawai muke tafkawa, jarumai da yawa na komawa harkar bude sana'o'i," in ji jarumin.

A 'yan kwanakin nan dai wasu manyan jaruman fina-finan Hausan suna ta faman kokarin samun hanyar da zasu fadada samun kudinsu.

Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya bude wani katon shagon sayar da kayan sawa a jihar Kano, inda Yakubu Muhammad da Sani Danja suka bude shagon daukar hoto.

KU KARANTA: Labari mai dadi: An sanya hannu akan dokar bayar da izinin zama a Saudiyya har Illa Masha Allah

Zaharadden ya bayyana cewa: "Naji labarin cewa gwamnatin kasar nan na shirin yiwa masana'antar nan wani abu, ni dai shawara ta a nan ita ce, ka da bai wa wasu tsiraru daga cikin mu kudi, saboda hakan ba zai sa matsalar masana'antar ta tafi ba, sai dai kawai idan ana so a azirta wasu 'yan kalilan daga cikin mu," kamar yadda jarumin ya shaidawa jaridar Premium Times.

Jarumin ya kara da cewa duk lokacin da aka bayar da kudi masu yawa irin wannan, wasu mutane ne 'yan kalilan za su kwashe kudin domin wata bukata tasu ta kansu.

Sannan ya roki gwamnatin kasar nan akan ta gina gidan kallon fim a arewacin kasar nan.

Tuni dama jaruman masana'antar mata irinsu Rahama Sadau da Hadiza Gabon suka fara sana'ar saida kayayyakin kwalliya da kuma yiwa kamfanoni tallace-tallace.

Inda wasu jaruman irinsu Adam Zango suka mai da himma wurin yin wakoki da kuma shirya taro a lokutan bukukuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel