Labari mai dadi: An sanya hannu akan dokar bayar da izinin zama a Saudiyya har Illa Masha Allah

Labari mai dadi: An sanya hannu akan dokar bayar da izinin zama a Saudiyya har Illa Masha Allah

- Dokar bayar da izinin mutum ya zauna a kasar Saudiyya har Illa Masha Allahu ta fara aiki

- Sannan kuma kasar ta shigo da wani sabon tsari da zai bai wa mutum damar zama a kasar na tsawon shekara daya kacal

- A yanzu haka dai an bude shafin yanar gizo ga masu bukatar cika wannan zama a kasar, inda zasu shiga su cika kuma su biya kudin da ake bukata

Kasar Saudiyya ta game yanke hukunci akan dokar da za ta bai wa mutanen da ba 'yan kasar ba damar zama a cikin kasar na iya tsawon rayuwarsu, ga duk wanda ke da bukatar hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya (SPA) shine ya ruwaito hakan a rubuce, inda ya bayyana cewa daga yau dokar bai wa mutane da ba 'yan kasar Saudiyya ba damar zama a Saudiyya har iya tsawon rayuwarsu za ta fara aiki, sannan kuma akwai wata hanya da mutum zai bi domin zama a kasar har na tsawon shekara daya.

Hakazalika an cire dokar da ta ke nuni da cewa dole sai mutum ya gabatar da garanto kafin ya samu damar zama a kasar ta Saudiyya.

KU KARANTA: Akwai sauran rina a kaba: Da gangan aka yi magudi a zaben jihar Kano - Tarayyar Turai

Rahoton ya bayyana cewa tuntuni an bude shafin yanar gizo wanda mutum zai iya shiga ya cika sannan ya biya kudin da aka bayyana domin wannan bukata.

Ga mutanen da suke da burin zama a kasar na har abada za su biya Riyal Dubu Dari Takwas (Dalar Amurka Dubu 213), sannan ga mutanen dake da bukatar zama na tsawon shekara daya za su biya Riyal Dubu Dari (Dalar Amurka Dubu 27).

Sai dai kuma izinin bai wa mutum damar zama a kasar Saudiyya na tsawon rayuwa ba yana nufin mutum ya zama dan kasa bane, amma duk wanda ya samu wannan damar yana da ikon shiga da fita daga kasar ta Saudiyya a duk lokacin da ya ga dama, sannan kuma yana da damar mallakar dukiya da kuma gabatar da kasuwanci a kasar.

'Yan uwan wanda ya samu izinin zama a kasar zamu iya karuwa ta kowanne bangare, sannan kuma samun biza zuwa kasar mai tsarki zai zo musu da saukin gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel