Masana kimiya sun ce ma’auratan da ke yawan fada na matukar son junansu
Masana kimiya sun ce ma’auratan da ke yawan samun sabani a tsakaninsu na matukar son junansu.
A cewar wani bincike da aka gudanar, an tattaro cewa kaso 44 cikin 100 na ma’auratan da ke fada sama da sau daya a mako guda yana taimaka masu sosai wajen gina soyayya da shakuwa mai dorewa.
Hasashe sun nuna cewa ma’auratan da ke yawan cece-kuce a tsakaninsu sun fi son kasancewa tare, domin duk da yawan sabanin da ke shiga tsakaninsu sun san cewa suna kaunar junansu matuka kuma da gaskiya.
Rikicin ma’aurata na taimaka masu wajen fahimtar juna, domin hakan zai sa kowa ya fahimci hakikanin abunda ke zuciyar dan uwansa ta yadda zai gyara. Ta haka ne za ka san abunda ke saurin hassala abokin zamanka.
KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa tayi karin haske akan lokacin da Buhari zai haramta almajiranci
Sabani tsakanin ma’aurata na sa su sauraron junansu da kunnen basira, saboda tattaunawa na daya daga cikin hanyoyin samun mafita ga kowani lamari.
Ta haka ne ma’aurata ke kara sanin junansu da kuma fahimtar halayyar juna domin mutum ya fi fallasa sirrin zuciyarsa a lokacin da yake cikin fushi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng