Abubuwu 25 da Buhari ya yi alkawarin zartarwa a mulkinsa zagon na biyu

Abubuwu 25 da Buhari ya yi alkawarin zartarwa a mulkinsa zagon na biyu

A ranar 29 na watan Mayun 2019 ne shugaban kasa Muhammad Buhari ta mataimakinsa Yemi Osinbajo suka karbi rantsuwar kama aiki na shugabancin Najeriya karo na biyu bayan lashe zaben da aka gudanar a watan Fabrairu.

Gabanin zaben, shugaban kasar ya rika yi wa al'ummar Najeriya alkawurran irin abubuwan cigaba da more rayuwa da zai yi musu idan sun zabe shi karo na biyu. Hakan dama al'adar 'yan siyasa ne musamman lokacin da ake yakin neman zabe.

Ga jerin wasu abubuwa 25 da shugaba Buhari ya yi alkawarin yi a mulkinsa zango na biyu.

1. Shigar da Najeriya mataki na gaba wato 'Next Level'.

2. Daukan matasa miliyan 1 karkashin shirin N-Power.

3. Bawa 'yan Najeriya miliyan 10 horo kan sana'o'i daban-daban.

4. Bawa manoma miliyan 1 ayyuka da tallafi karkashin shirin bawa manoma bashi 'Anchors borrowers scheme'.

5. Samar da ayyuka miliyan 1.5 ta hanyar kiwo dabobi, shanu da shuka.

6. Samar da ayyuka miliyan 5 ta hanyar noman zamani.

7. Ware kudi dallan Amurka miliyan 500 domin fanin fasaha da kirkire-kirkire da samar da ayyuka 500,000.

8. Bawa matasa 200,000 horo kan samun ayyuka a fanin fasahar intanet da nishantarwa.

9. Kirkiran biranen hada-hadar kasuwanci da kamfanoni 6 a shiyoyin kasar 6.

10. Kara adadin 'yan makaranta da ake ciyarwa daga miliyan 9.3 zuwa miliyan 15.

DUBA WANNAN: Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

11 . Samar da karin ayyuka 300,000 ga masu daffa abincin 'yan makaranta da manoma

12. Kammala layin dogo daga Legas zuwa Calabar, kammala gadar 2nd Niger, Tiitin East West, Titin Abuja - Kaduna - Zaria da sauransu.

13. Kammala layin dogo daga Ibadan zuwa Kano, Port Harcourt zuwa Maiduguri da sauransu.

14. Fadada sabis din yanar gizo ta hanyar shimfida fibre network mai tsawon kilo mita 120,000.

15. Kara adadin wutar lantarki da Mega Watt 1000 duk shekara.

16. Inganta rabar da wutan lantarki zuwa Mega watt 7000; zuwa jami'o'i 9, kasuwanni 300 da wasu wurare.

17. Kaddamar da aikin samar da lantarki a kauyukka da kudi dallan Amurka miliyan 550.

18. Bayar da bashi mara ruwa na naira miliyan 1 ga masu sana'o'in hannu.

19. Kara adadin masu amfana da Tradermoni daga miliyan 2.3 zuwa miliyan 10.

20. Kafa ofisohin hukumomin sanya idanu kan kayayaki irinsu (CAC, NAFDAC, SON da sauransu.)

21. Sake bawa malaman frimari da sakandari na gwamnati horo.

22. Sake tsarin makaruntu 10,000 a duk shekara

23. Tallafawa al'umma wurin biyan wani kaso na kudin inshoran lafiya.

24. Dauke nauyin biyan kudin inshoran lafiya ga kashi 40 cikin 100 na mutanen da suka fi talauci a kasar.

25. Kara fadada shirin bayar da lafiya bai daya daga 12.6% zuwa 45% a shekarar 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel