Yadda wani lauya ya ciji yatsar budurwarsa yayin musayar yawu

Yadda wani lauya ya ciji yatsar budurwarsa yayin musayar yawu

An shaida wa wata babban kotun Abuja da ke zamanta a Apo ta yadda wani lauya mazaunin Abuja ya datse karamin yatsar matar da zai aura yayin da suka samu sabani.

Ofishin Attorney Janar na kasa tana tuhumar lauyan , Emmanuel Omattah mazaunin Shagari Dei-Dei a Abuja da laifin da aikata laifuka takwas masu alaka da duka, yiwa wani rauni, barazana da yaudara.

Ana zarginsa da yi wa tsohuwar budurwar da zai aura, Elsie Imaikop duka, yaga mata tufafi da lalata motar ta kirar Toyota Camry.

Amma Omattah bai amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

DUBA WANNAN: Na yi tiyata fiye da 500 kuma babu wanda ya mutu - Likitan bogi da aka kama a Adamawa

A zaman kotun da aka yi a ranar Alhamis, Imaikop ta shaidawa kotu cewa lamarin ya faru ne saboda ta kallubalance shi kan katin aurensa da ta gani da wata macen daban.

Imaikop ta fadawa kotu cewa 'yar uwar Omattah ne ta sanar da ita cewa ya samu wata budurwar da zai aura ba ita ba.

"Ban yarda da abinda ta fada min ba sai da na ga hotunnan auren gargajiya da su kayi a shafin sada zumunta.

"Da na gano an tsayar da ranar auren su, sai na sanar da faston cocin mu.

"A ranar da nayi karar sa wurin faston mu sai ya zo gida na dauke da adda ya yi barazanar zai kashe ni.

"Ya cije dan 'yantsa na lokacin da na ke kokarin kare kaina," inji ta.

Imaikop ta shaidawa kotun cewa sun fara soyaya ne tun 2012 kuma ya yi alkawarin zai aure ta.

Ta ce ta bayar da gudunmawa wurin karatunsa da ya yi a makarantar koyan aikin lauya.

Daga karshe, alkalin kotun, Justice Silvanus Oriji ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel