Na yi tiyata fiye da 500 kuma babu wanda ya mutu - Likitan bogi da aka kama a Adamawa

Na yi tiyata fiye da 500 kuma babu wanda ya mutu - Likitan bogi da aka kama a Adamawa

Ibrahim Mustapha, wani likitan bogi kuma shugaban Cottage Hospital, Fufore da ke jihar Adamawa ya shiga hannun jami'an 'yan sandan farar hula (DSS) bisa zarginsa da sanadin mutuwar masu jinya saboda kasancewarsa likitan bogi.

An ce ya yi tiyata fiye da 500 inda ya yi sanadiyar rasuwar kimanin masu jinya 46 daga watan Janairu zuwa Mayun 2019.

A yayin da ake bajekolinsa ga manema labarai a ranar Alhamisa a Yola, Dirktan DSS na jihar, Bola Olori ya ce jami'an sa "sun kama wani Ibrahim Mustapha da ya dade yana aiki a matsayin babban likita a Furfore Cottage Hospital da ke karamar hukumar Fufore na jihar Adamawa."

DUBA WANNAN: Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

Mr Olori ya ce binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa Mustapha yana da takardan satiket na kammala sakandare ta National Board of Technical Education (NBTE).

Tsohon likita mai tiyatan ya amsa cewa takardun kammala karatun likitan da ya gabatarwa asibitin na bogi ne amma ya musanta cewa ya taba yin sanadin rasuwar ko da mai jinya daya ne a tsawon lokacin da ya ke aiki.

"Eh, na nemo takardan karatun likita ta bogi kamar yadda Direktan DSS ya fadi amma nayi manya da kananan tiyata da suka hada da tiyatar haihuwa da sauransu kimanin 500 amma babu mai jinya da ya taba mutuwa kamar yadda aka ce."

Hukumar ta DSS ta ce, "Ya koyi aikin likitancin ne lokacin a yayin da ya yi aiki a Gombe a asibitoci da dama a matsayin mai kula da dakin masu jinya. Wani likita ne ke taimaka masa inda ya bashi sakamakon jarrabawar NECO da sakamakon kammala karatun likita na Jami'ar Bayero da ke Kano da takardar kammala NYSC da satifiket na kungiyar Likitocin Najeriya da sabunta lasisi.

"Wanda ake zargin ya samu aiki ne da gwamnatin jihar Adamawa a matsayin likita a Oktoban 2015 inda daga bisani ya kai matsayin babban likita kuma yana aiki a Cottage Hospital a Mayo-Belwa da Fufore."

Asirinsa ya tonu ne da ya tafi amsa tambayoyi a matsayinsa na likita cikin tawagar likitocin da za su tafi aikin hajji na 2019.

Wani mutum da ya san shi a matsayin ma'aikaci mai kula da dakin masu jinya a wani asibiti a Gombe ne ya tona shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel