Gwamna Umahi zai zamo shugaban Najeriya a 2023 - Miyetti Allah
Kungiyar makiyaya ta Fulani, Miyetti Allah, ta shimfida goyon bayan ta a kan kasancewar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, magajin kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
A yayin babban taro na musamman da aka gudanar a kan harkokin tsaro na yankin Kudu maso Gabas cikin birnin Enugu, kungiyar Miyetti Allah babu ko tantama ta ce gwamna Umahi ne zai ci gajiyar kujerar shugaban Najeriya a 2023.
Jagoran kungiyar na kasa baki daya, Alhaji Muhammad Kirowa, shi ne ya bayar da wannan shaida da cewar al'ummar Najeriya su kasance cikin shirin karbar gwamna Umahi a matsayin shugaban Najeriya yayin da Buhari ya kammala wa'adin sa a 2023.
Alhaji Kirowa wanda sakataren kungiyar Miyetti Allah na kasa, Baba Othman Ngalzarma ya wakilta a babban taron, ya ce kasancewar gwamna Umahi jagoran kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Gabas, ya taka rawar gani wajen kulla kyakkyawar dangarta tsakanin Fulani makiyaya na yankin da kuma takwarorin su na yankin Kudu maso Yamma.
Tamkar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kungiyar Miyetti ta yaba da kwazon gwamnan na jihar Ebonyi dangane da rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakankanin kungiyar Miyetti Allah a reshen ta na yankunan biyu.
KARANTA KUMA: Matan Najeriya 110 na mutuwa a kullum yayin haihuwa - UN
Da yake gabatar da na sa jawaban, gwamna Umahi yayin yabawa kwazon hukumar 'yan sanda wajen tsayuwa a kan tabbatar da ingataccen tsaro, ya kuma nemi 'ya'yan kungiyar Miyetti Allah da su yi riko da al'adun Fulani wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin su da Manoma.
Kazalika wani kwamishinan hukumar 'yan sanda, Tommy Mom, ya yabawa gwamnonin Kudu maso Gabas a kan tsayuwa da kuma jajircewa wajen ganin tsaro ya inganta a jihohin da suke jagoranta.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng