Kwamishinan 'yan sanda: Yadda makiyaya ke amfani da dabbobi suna boye bindigogi

Kwamishinan 'yan sanda: Yadda makiyaya ke amfani da dabbobi suna boye bindigogi

- Hukumar 'yan sanda ta gano wata hanya da makiyaya ke bi suna boye bindigogi a jikin shanaye

- Hukumar ta kuma sanar da yadda makiyayan ke sayo bindigogi suna shigo dasu cikin gida Najeriya, daga kasashen dake makwabtaka da Najeriya

- Ta kuma sanar da yadda makiyayan ke bin barauniyar hanya domin kaucewa hukumomin tsaro dake tsayawa a bakin iyaka

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Adamawa, Audu Adamu Madaki, ya bayyana yadda makiyaya suke amfani da shanunsu suna boye muggan makamai, kuma suna samun damar yawo da su a duk inda suke so a fadin kasar nan.

A lokacin da yake magana akan matsalar tsaro da kuma matsalar garkuwa da mutane dake addabar mutanen jihar, jiya Laraba a garin Yola babban birnin jihar, Madaki ya bayyana cewa mutane uku wanda suka kama da AK47 guda biyu sun bayyana masa yadda suke boye bindigun a jikin dabbobinsu su shigo dasu Najeriya daga kasar Kamaru.

"Makiyayan sun bayyana mini cewa suna boye bindigun a cikin buhu ne sai su daure a jikin shanayen, hakan zai basu damar zuwa duk inda suke so ba tare da wata matsala ba."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dan gidan ministan Buhari yasha dakyar daga hannun 'yan bindiga

"Sannan sun sanar dani cewa suna sayo bindigogin daga kasar Kamaru ne su shigo dasu Najeriya daga cikin daji, domin su kaucewa jami'an tsaro dake tsayawa akan iyaka."

Sannan kuma kwamishinan yayi magana game da matsalar makarantun allo na kananan hukumomi guda bakwai dake cikin jihar.

A cewarsa 'yan sanda sun gano wasu makarantun allo a kananan hukumomin Jada, Song, Gombi, Mubi North, Yola North, da kuma Fufore.

"Akwai alamar tambaya kaga mutum kato dashi yana zuwa makarantar allo, saboda nima nayi makarantar allo lokacin ina dan shekara bakwai. To ni na kasa gane yadda baligin mutum sa'a na zai ce zai dinga zuwa makarantar allo," in ji shi.

Kwamishinan kuma ya gabatar da wasu mutane 86 da aka kama su da laifin garkuwa da mutane, fashi da makami, fyade da sauran manyan laifuka a cikin garin Yola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel