Hanyoyi 5 da za a iya amfani da ganyen Kabeji wajen maganin wasu manyan cututtuka

Hanyoyi 5 da za a iya amfani da ganyen Kabeji wajen maganin wasu manyan cututtuka

- Ganyen Kabeji na da matukar alfanu a jikin mutum

- Yana dauke da sinadarin 'Protein' da 'Vitamin C' wanda dan Adam ke bukata matuka wajen karfafa garkuwar jikinsa

- Kabeji na wasu cututtuka zama a jikin mai yawan cin sa

Ganyen Kabeji na daya daga cikin kayan lambu da mutane ke yawan amfani dashi, musamman a cikin abinci ko kuma kwadon shi da kuli.

Da yawan mutane suna cin wannan ganye ne don marmari ba tare da sun san tarin alfanu da yake dashi ba wajen magance wasu cututtuka a jikin dan Adam.

Kabeji na dauke da sinadarin ‘Protein’ wanda ke gina jiki, da kuma 'Vitamin C' wanda ke warkar da cututtuka a jiki dan Adam.

Ga hanyoyi 5 da za a iya amfani da wannan ganye wajen magance wasu manyan cututtuka

1. Ganyen Kabeji na kashe kwayoyin cuta da ke shiga cikin budadden ciwo:

Za a daddaka ganyen sai a murza a saman ciwon. Yin haka na taimakawa matuka wajen kashe kwayoyin cuta da ka iya shiga cikin ciwon.

2. Kabeji na warkar da ciwon nono da tsayar da ruwan nono ga macen da ta gama shayarwa:

Ga matan da suka cire ‘ya’yansu daga bakin nono, ganyen kabeji na taimakawa wajen hana ciwon nono ya kuma hana zuban ruwansa bayan yaye.

Mace za ta dauki ganyen ta lullube nononta da shi da daddare sannan ta cire ganyen washe gari.

3. Kabeji na maganin gyambon ciki:

Ga mutummai fama da atsalar gyambon ciki , sai ya lazmci cin ganyan kabeji danye wanda aka yi kwadon shi da kuli ko kuma dafaffe a cikin shinkafa ko fate ko kuma ya sharuwan ganyen kabejin.

KU KARATA KUMA: Jami’an tsaro sun cafke wadanda su ka sace Amarya a Dajin Falgore

4. Kabeji na hana saurin tsufa:

Yawan cin kabeji ko kuma wanke fuska a ruwansa na hana tsufa da wuri.

5. Ganyen Kabeji nakawar da ciwon kai:

Kafin a kwanta da daddare sai a tsinki ganyen kabeji a lullube kai da shi. Yin haka zai hana ciwon kan da ake ji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng