Hamshakan mata 5 da 'karan su ya kai tsaiko' a Najeriya

Hamshakan mata 5 da 'karan su ya kai tsaiko' a Najeriya

Najeriya kasa ce da ke da mata masu jarumta da kwazo a fanoni daban-daban da suka hada da siyasa, tattalin arziki da ayyukan raya kasa.

Wadannan matan sun zama 'kalabi cikin rawwuna' duba da cewa maza sun fi mamaye galibin harkokin jan ragamar kasar. Wasu daga cikin matan sun zama abin alfahari da kwatance a gida Najeriya da kasahen waje.

Ga wasu daga cikin su:

1 - Folorunso Alakija: 'Yar kasuwa mai shekaru 68 da haihuwa tana daya daga cikin hamshakan matan Najeriya. Tayi fice a fashin man fetur, sarrafa tufafi da fannin buga jaridu. Alakija ita ke biye da Ngozi Okonjo-Iweala cikin jerin mata hamshakan matan Afirka na jaridar Forbes a 2015. Itace mace ta 80 a jerin hamshakan matan duniya a 2016 inji Forbes.

Ita ce shugaban The Rose of Sharon Group da ya kunshi The Rose of Sharon Prints & Promotions Limited and Digital Reality Prints Limited kuma itace mataimakiyar shugaban Famfa Oil Limited.

2 - Ngozi Okonjo-Iweala: Kwarariyar mai nazarin tattalin arziki da tsare-tsare tayi suna a duniya, tana cikin kwamitin direktoci na musamman na Standard Chartered Bank da Twitter da Global Alliance for Vaccines and Immunisation (GAVI) da African Risk Capacity (ARC).

Iweala tayi ministan kudi sau biyu a Najeriya. An haife ta ne a ranar 13 ga watan Yunin 1954.

Dakta Iweala ta samu lambobin yabo masu dimbin yawa a gida Najeriya da kasahen waje da suka sanya ta jerin matan da suka fi fice da jarumtaka a duniya.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan bindiga ke cin karen su ba babbaka a Katsina - Sanata

3 - Aisha Buhari: Uwar gidan shugaban Najeriya kwarariya ce a fannin gyarar fata da kwaliya sannan marubicya ce wadda ake amfani da litaffin ta a wurin koyar da dalibai a karkashin National Basic Technical Education (NBTE).

An haife ta ranar 17 ga watan Fabrairun 1971. Tana da zauren gyarar jiki mai suna Hanzy Spa da makarantar koyar gyarar jiki mai suna Hanzy Beauty Institute a Kaduna da Abuja amma ta rufe zauren gyarar jikin bayan mijinta ya zama shugaban kasa a 2015.

Ta mayar da hankali kan ayyuka da suka hada da kare hakokin yara da mata. Ta kasance cikin wadanda ke neman ganin yara mata sunyi makaranta kafin ayi musu aure, tana daga cikin wadanda ke ganin bai dace a yi wa yara aure ba kafin su kai shekaru 17.

4 - Amina Mohammed: An haife ta a ranar 27 na watan Yunin 1961 kuma ita ce Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a yanzu kuma a baya ta rike mukamin Ministan Muhalli na Najeriya.

Amina tana aiki tare da shugabanin duniya wurin ayyukan taimakon al'umma da suka hada da yaki da dumamar yanayi, kula da lafiyar mata, kawo sauyi a tsare-tsaren mulki a kasashen duniya da inganta lafiyar mata da yara.

5 - Ibukun Awosika: Tana daya daga cikin 'yan kasuwan Najeriya da su kayi fice a fannin da maza su kayi dafifi.

Ta mallaki kamfanin kera kayayakin adon daki mai suna Quebees da aka kafa a 1989 daga bisani kamfanin ya canja suna zuwa 'The Chair Centre Limited' wadda daya ne cikin manyan kamfanonin sarrafa kayan adon gida a Najeriya.

Ibukun ta taka muhimmiyar rawa wurin inganta tattalin arzikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel