Za mu nada 'yan adawa jagoranci a majalisar wakilai - Gbajabiamila

Za mu nada 'yan adawa jagoranci a majalisar wakilai - Gbajabiamila

Sabanin furuci da kuma akidar shugaban jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole, na cewar babu wani dan jam'iyyar adawa da zai samu jagorancin kowane kwamiti a sabuwar majalisar Tarayya, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce ba za ta sabu ba.

Kakakin majalisar wakilai ta tara a tarihin dimokuradiyyar Najeriya, Honarabul Femi Gbajabiamila, ya ce babu shakka sabuwar majalisar sa ba za ta mayar da 'yan jam'iyyar adawa saniyar ware ba wajen nadin mukamai na jagorancin wasu kwamitai.

Bayan karin haske na cewar sunayen jagororin kwamitai daban daban za su bayyana nan ba da jimawa ba, kazalika kakakin majalisar ya ce zai kawo sabon sauyi na tsare-tsare a majalisar domin inganta ci gaba da kuma nagarta sabanin yadda ta kasance a baya.

Furucin Gbajabiamila ya zo ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a fadar Villa bayan ganawar sa da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo. Ya ce ganawarsu ta gudana da manufa ta tumke damarar bunkasa tattalin arziki da kuma fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Legit.ng ta fahimci cewa, akidar Gbajabiamila ta baiwa 'yan jam'iyyar adawa damar jagorantar wasu rukunai a majalisar wakilai na cin karo da kudirin da shugaban jami'yyar APC na kasa ya raja'a a kai.

KARANTA KUMA: Harin kunar bakin wake: Buhari ya aika da sakon jaje jihar Borno

Ana iya tuna cewa, Oshiomhole yayin wata liyafar dare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiryawa zababbun 'yan majalisar Tarayya, ya ce 'yan jami'yyar adawa a wannan karo ba za su samu damar numfasawa ba wajen rike mukamai sabanin kuskuren da jam'iyyar APC ta tafka a 2015.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Honarabul Gbajabiamila ya zamto sabon kakakin majalisar wakilai ta tara bayan lallasa abokin adawar sa, Honarabul Umar Bago, yayin zaben shugabannin Majalisar Tarayya da aka gudanar a makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng