Ko ina akwai na Allah: Wani mutumi ya bayyana yadda Fulani suka kubutar dashi daga hannun masu garkuwa da mutane

Ko ina akwai na Allah: Wani mutumi ya bayyana yadda Fulani suka kubutar dashi daga hannun masu garkuwa da mutane

- Wani saurayi ya bayyana yadda wasu Fulani Makiyaya suka ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane

- Saurayin yaa ce gaskiyar lamari bai kamata a dinga kallon Fulani a matsayin 'yan ta'adda ba, ganin yadda suka ceto su ba tare da sun karbi koda sisin kwabo a hannunsu ba

- Saurayin ya bayyana cewa mutanen da suka sace su ko kadan basu yi kama da Fulani ba, hasali ma Fulani ne suka ceto su daga hannunsu

Wani mutumi dan Najeriya ya bayyana yadda wasu Fulani Makiyaya suka kubutar dashi tare da dan uwansa daga hannun wasu miyagun masu garkuwa da mutane a jihar Ondo.

A cewar mutumin, barayin sun yi garkuwa da sune lokacin da suke kan hanyar Iwo-Ifon, wadanda ko kadan basu yi kama da fulani ba a jihar ta Ondo.

Mutumin ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter ne, inda ya ce:

"Bari na bayyana muku irin halin dana shiga kwanaki biyu da suka wuce a jihar Ondo. Ku saurare ni kuji, ban san yadda aka yi labarai ke yaduwa na cewa Fulani makiyaya suna satar mutane akan manyan hanyoyin kasar nan, gaskiyar magana ba Fulani bane.

"Hakan ya faru kwanaki biyu da suka gabata akan hanyar Owo-Ifon dake jihar Ondo, mun fara tafiyar mu da misalin karfe 7 na safe, don zuwa Ipele, muna cikin tafiya sai muka ga wasu mutane su hudu sun fito daga daji.

"Suka sanya itace akan hanyar mu, kuma suka bukaci dukanmu mu fito daga motar, kuma kafin mu fara tafiyar Kawun mu ya fada mana irin yadda satar mutane ya zama ruwan dare a kasar nan.

"Kowannen su dauke yake da manyan bindigu, kuma ko kadan wadannan mutane basu yi kama da Fulani ba.

KU KARANTA: Allah wadan naka ya lalace: Wata mata ta tona asirin aminin mijinta da ya bukaci yin zina da ita

"Sun ja mu zuwa wata fadama, sai daya daga cikinsu yace zai je ya dawo, suka rage saura su uku. Sai muka zauna domin mu huta dukan mu hannayen mu a daure. Na riga na gama yin addu'o'i na.

"Sai suka fara tambayar mu ko akwai wanda zasu kira domin ya zo ya fanshe mu, kar ku manta har yanzu bamu isa sansaninsu ba, muna gurin fadamar nan. Cikin ikon Allah sai naga wani karamin yaro wanda bai fi shekara goma ba a duniya, yana ganin mu sai ya gudu.

"Dan uwansun na dawowa muka cigaba da tafiya har muka iso sansaninsu. Shugabansu na wurin a zaune tare da wasu mutane biyar wadanda suka sato sun daure su a jikin bishiya.

"Wani ikon Allah ashe yaron nan dana gani ba guduwa yayi ba, ya biyo mu a hankali a baya ne. Bayan mun shafe kusan awa uku muna shan bakar azaba a hannunsu, sai ga yaron nan yazo tare da Fulani 'yan uwanshi guda bakwai.

"Suna zuwa suka kwace bindigogin barayin suka kuma harbe biyu daga cikinsu, suka sake mu. Sauran barayin suka gudu tare da shugaban su.

"Haka suka taimaka mana har muka dawo wajen motar mu. Haka muka karasa kauyen da zamu je, Kawun mu shine ya bayyanawa mutane duka abinda ya faru, saboda ni tsoro ya hanani yin magana.

"Sai dana kwana daya kafin hankalina ya dawo jikina. Ban san yadda barayin suke ba a wasu yankunan na kasar nan, amma gaskiyar magana shine mu wadanda suka sace mu ba Fulani bane. Fulani da ake ta faman zargi sune ma suka ceto mu daga hannun barayin."

Matsalar garkuwa da mutane dai taki ci taki cinyewa a Najeriya, duk da irin kokarin da jami'an tsaro suke yi na ganin sun kawo karshen abin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng