Farin ciki ko ta ina bayan Ustaziya ta zama Gwazon shekara a UNIABUJA

Farin ciki ko ta ina bayan Ustaziya ta zama Gwazon shekara a UNIABUJA

Labari ya iso gare mu cewa a na ta faman murna da farin ciki a jami’ar tarayya da ke Abuja watau UNIMAID bayan da wata Baiwar Allah ta kammala karatu a matsayin gwarzon wannan shekarar.

Wata ‘Daliba da ta kammala karatu daga sashen kimiyya ita ce ta ciri tuta a zangon karatu na bana inda ta kare jami’ar ta Abuja da maki 4.82. Sunan wannan Baiwar Allah Talatu Adamu.

Kamar yadda wani Matashi wanda ya ke jami’ar mai suna Abdulhameed Nuhu Omeiza (wanda ake fi sani da Abu Jandal) ya sanar, Talatu ita ce gwarzon UNIABUJA na shekarar 2018/19.

KU KARANTA: Mata su na so Buhari ya tafi da su a Gwamnatin APC

Farin ciki ko ta ina bayan Ustaziya ta zama Gwazon shekara a UNIABUJA
Talatu Adamu ce Gwazon shekarar nan a Jami'ar Abuja
Asali: Twitter

A kwanan nan ne jami’ar ta yaye ‘Daliban da su ka kammala karatu a biki na 23 da aka shirya. Talatu ta na cikin jami’n kungiyar MSSN na Musulunci da ke wannan jami’a da ake ji da ita.

Malam Abdulhameed Nuhu Omeiza ya ke cewa nasarar da Talatu ta samu ya nuna cewa akwai riba wajen riko da addini da kuma dagewa da kwazo da bada himma wajen neman abin Duniya.

Kwanakin baya ne kuma aka samu wani Matashi mai suna Nuhu Ibrahim wanda ya doke duk wani tarihi da aka kafa a jami’ar ABU ta Zariya inda ya kammala Digirinsa da maki 4.94.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel