Allah mai iko: Pogba ya bayyana dalilan da suka sa ya shiga addinin Musulunci

Allah mai iko: Pogba ya bayyana dalilan da suka sa ya shiga addinin Musulunci

- Shahararren dan wasan kwallon kafa na Manchester United ya bayyana dalilin shigar shi addinin Musulunci

- Ya bayyana cewa abokanshi ne suka dinga kwadaitar dashi addinin har yaji yana son shi

- Rahotanni sun nuna cewa mahaifiyar dan wasan Musulma ce, yayin da ya taso ba a musulmi ba

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa na Manchester United, Paul Pogba ya bayyana dalilan da ya sanya shi shiga addinin Musulunci a lokacin da yake dan shekaru ashirin a duniya.

Duk da cewa mahaifiyar Pogba musulma ce, amma shi bai tashi cikin addinin Musulunci ba, amma dan wasan bayan ya juya zuwa addinin na Musulunci yana halartar aikin hajji zuwa kasa mai tsarki wato Makkah a lokutan Hajji da kuma cikin watan Ramadana.

Pogba ya bayyanawa 'yan jarida dalilin shigar shi addinin musulunci a lokacin da yayi hira da su, inda ya bayyana cewa yaji nutsuwa ta zo mishi a lokacin da ya taba yin sallah da wasu abokanansa musulmai.

KU KARANTA: Wa'iyazubillah: An kama malamin jami'a tsirara yana kokarin yin zina da dalibarshi

"Hakan ya faru saboda ina da abokai Musulmai da yawa, kuma muna yawan zama muyi hira tare da su.

"Na zauna ina ta faman yiwa kai na tambayoyi, sai kuma na fara gabatar da bincike da kaina.

"Na taba yin sallah da abokaina sau daya kuma naji canji sosai a tattare dani.

"Tun daga lokacin na cigaba da yin sallah, dole sai kayi sallah sau biyar a rana idan har ka cika Musulmi na gari, saboda sallah tana daya daga cikin gishikin musulunci.

"Gaskiya addinin musulunci ya canja ni matuka, saboda yana sani ina yin tunanin lahira a koda yaushe," in ji Paul Pogba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel