Yadda Tinubu da shugabannin kabilar Yoruba suka ci amanar Abiola a 1993 - Sule Lamido

Yadda Tinubu da shugabannin kabilar Yoruba suka ci amanar Abiola a 1993 - Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wani shugaba ko guda daya daga cikin shugabannin kabilar Yoruba da ya taimaki marigayi Mashood Abiola a nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 da aka soke.

Lamido ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan mayar da ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar dimokradiyya a Najeriya.

Ya ce dukkanin shugabannin kabilar Yoruba sun tare ne a jam'iyyar NRC saboda suna ganin MKO Abiola a matsayin mutumin da ya fi kusanci ga 'yan arewa, ya ce hakan yasa suka ki zabar sa a wancan lokacin.

"Kamar abinda ya faru a shekarar 1999 ne da shugabannin kabilar Yoruba suka ki goyon bayan Olusegun Obasanjo, sai bayan ya samu nasara a zabe sannan suka fara kaunar sa," a cewar Lamido.

DUBA WANNAN: Masana sun gano tsadar tufafin da Aisha Buhari ta saka yayin bikin ranar dimokradiyya

Lamido ya bayyana cewar dukkan shugabannin jam'iyyar APC na yanzu har da shugaba Buhari sun taka mummunar rawa ne a tarihin ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.

"Babu wani daga cikin shugabannin APC da za a iya kiransa da gwarzon ranar 12 ga watan Yuni idan ka cire sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shine shugaban jam'iyyar SDP na jihar Adamawa a wancan lokacin.

"Babu yadda za a yi makiyin dimokradiyya ya iya zama hadimin dimokradiyya," a cewar sa.

Tsohon gwamnan ya bayyana Buhari a matsayin makiyin siyasa da bai taba yin hobbasa wajen kare dimokradiyya ba a Najeriya.

"Buhari ne ya yi wa gwamnatin dimokradiyya ta Shehu Shagari juyin mulki," a cewar Lamido.

Lamido ya bayyana cewar shugaba Buhari ya karrama ranar 12 ga watan Yuni domin neman suna kawai, tare da bayyana cewar ya na daga cikin suka taka mummunar rawa a tarihin ranar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel