Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a jihar Neja

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a jihar Neja

- Sama da mutane 70 'yan bindiga dadi suka kashe a jihar Neja

- Sun kuma yi awon gaba da sama da shanu dari takwas

- An bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaiwa mutanen da abin ya shafa dauki

'Yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare akan wasu kauyuka na karamar hukumar Shiroro, dake jihar Neja, a jiya Alhamis dai 'yan bindigar sun kashe sama da mutane 70, inda wasu karin kauyuka guda takwas suke fuskantar barazanar 'yan ta'addar, haka kuma sama da mutane 1,000 sun gudu sun bar gidajen su.

Harin wanda aka fara kai shi ranar Lahadi 9 ga watan Yuni, 2019 an kashe kimanin mutane 12 a ranar, inda a yanzu haka 'yan ta'addar suke kara shiga wasu kauyuka don cigaba da kashe mutane babu gaira babu dalili.

Rahotanni sun nuna cewa an garzaya da mutane masu yawan gaske zuwa asibiti dake garuruwan, Kuta, Erena da Zumba, sannan da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa sun gudu sansanin 'yan gudun hijira dake kusa da kauyukan nasu.

KU KARANTA: Kunji fah: Gwaggon biri ya sace naira miliyan 10 a gidan Zoo din Kano

A wata hira da 'yan jarida suka yi da Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sanata David Umaru, wanda yankin sa yake fama da matsalar tsaron, ya bayyana cewa kimanin mutane 19 ne suka mutu a cikin kwanaki 6 a kauyen Kwaki, sannan mutane 14 sun mutu a Barden Dawaki.

Haka kuma rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane 8 a Ajatawyi, 7 a Gwassa, 5 a Ajayin Bataro, 4 a Bwailo, 3 a Baton, sai kuma mutum biyu a kauyen Giji, yayin da 'yan ta'addar suka yi awon gaba da shanaye sama da 800 na mutanen da abin ya shafa.

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP Mohammed Abubakar Dan-Inna, ya ce rundunar 'yan sandan tana da masaniya akan mutuwar mutum 12 ne kawai, sannan ya kara da cewa an tura jami'an tsaro yankunan da abin ya shafa.

Haka kuma, Sanata David Umaru ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaiwa mutanensa dauki daga hare-haren da 'yan ta'addar suke kai musu a duk lokacin da suka ga dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel