Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

Mutane da dama sun taba fadawa tarkon masu yada kudaden jabu saboda ba su iya banbance takardan naira mai kyau da jabu ba.

Idan hakan ya taba faruwa da kai ko kuma kana son yin takatsantsan don kaucewa bata-gari masu bawa mutane jabun nairori, ga wasu hanyoyi da za kayi amfani da su don banbance jabun kudi da mai kyau.

1 - Amfani da ruwa

Idan ba ka yarda da takardan naira da aka baka ba, hanya mai sauki na tabbatar da sahihancin ta shine jika hannun ka da ruwa sannan ka murza nairar, idan kaga launin jikin nairan ya fara zuba wanna alama ce ta jabu.

Idan hakan bai gamsar da kai ba, sai ka tsinduma nairar cikin ruwa na dakika 30, ka tabbatar ya jike sharkap, za ka ga launin yana zuba idan dai jabu ne.

DUBA WANNAN: Assha: 'Yar majalisa ta sha mari a hannun abokin aikin ta

2 - Lura da zare mai launin gwal

Takardan N1000 na da wani zare mai launin gwal kusa da saka hannun gwamnan CBN. Duk lokacin da ka ga zaren ya fice daga kudin toh kudin jabu ne.

N1,000 na asali, zaren baya fita duk yadda kayi kokarin ka cire shi.

3 - Amfani da fitilar haske na mercury

Akwai wasu alamu da ke jikin takardan naira da idanun mutum ba zai iya gani ba sai da taimakon hasken fitilar mercury.

Idan aka haska N1,000 da hasken mercury, zai nuna lamba N1,000 mai haske a jikin kudin. Amma idan jabun kudi ne, dukkan rubutun jikin kudin za su zama sama-a-kasa.

4. Lura da zaren da ke cikin takardan naira

Akwai wani zare da ke takardun naira mai kama da 'ribon' da ya fara daga sama zuwa kasa amma banda N50.

A takardar naira mai kyau, za ka ji zaren yana da kauri kuma an fi ganin sa da kyau a tsohon kudi.

Amma idan jabu ne za ka ga zaren ba shi da kauri kamar na mai kyau kuma idan ka sanya abu ka goge shi za ka ga yana zuba kamar abinda ake amfani da shi wurin rufe lambobin katin waya da ake gogewa.

5 - Yanayin laushin takardan nairar

Duk lokacin da ka rike takardan naira a hannu ka lura tayi laushi da yawa kuma hotunan jikin ta sunyi dusshi-dushi, kayi maza ka mayarwa wanda ya baka domin wannan alama ce ta jabun naira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel