Allah ya kyauta: Barayi sun ki sakin wani babban ma'aikaci bayan biyansu naira miliyan 50

Allah ya kyauta: Barayi sun ki sakin wani babban ma'aikaci bayan biyansu naira miliyan 50

- Wasu masu garkuwa da mutane sun ki sakin wani tsohon ma'aikacin gwamnati bayan sun karbi kudin fansa

- Iyalan mutumin sune suka hada naira miliyan hamsin suka bai wa masu garkuwa da mutanen, amma kuma suka ki sakin shi, da nufin sai an kara musu kudin fansar

- Wani dan uwan mutumin ya bayyana cewa sun shafe sama da wata daya basu kara jin duriyar dan uwan nasu ba

Dakta Sule Audu, tsohon ma'aikacin gwamnati ne wanda aka sace watanni biyu da suka gabata, kuma har yanzu yana hannun 'yan bindigar.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa iyalan tsohon ma'aikacin sun yi karo-karo a junansu suka hada naira miliyan 50 kudin fansa, domin a sako shi, amma wani abin bakin ciki barayin sun ki sakin shi.

Daya daga cikin iyalan Dr. Audu, wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce yanzu kusan sama da wata daya kenan basu kara jin duriyar mutumin ba, kuma duk da haka barayin suna bukatar a kara musu kudin fansa.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta je taro sanye da rigar miliyan 1.6

Haka kuma, wasu 'yan mata 'yan kabilar Jukun da wani lauya da wasu masu safarar shanaye guda uku, wadanda aka sace a wata biyu da suka gabata sun samu sun kubuta.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa mutanen sun samu sun kubuta ne daya bayan daya, bayan da 'yan uwansu suka biya kudin fansa.

Duka mutane bakwai din, kamar yadda muka samu rahoto, anyi garkuwa da sune akan hanyar Wukari zuwa Takum, wurin dama yayi kaurin suna akan sace mutane watannin da suka gabata.

An yi kokarin aji ta bakin mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, amma wayarsa a kashe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel