Aisha Buhari ta je taro sanye da rigar miliyan 1.6

Aisha Buhari ta je taro sanye da rigar miliyan 1.6

- Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta halarci wani taro tare da mijin nata sanye da wata riga mai dan karen tsada

- Rigar kamar yadda masa suka sanar ta kai dalar Amurka 4,290, kimanin Naira Miliyan daya da dubu dari shida

- Rigar ana yin ta a kasar Indiya ne, inda kuma ake sayar da ita a shagunan yanar gizo na kaya masu tsada

Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta sanya wata riga mai kama da abaya wadda kiyasin kudin ta ya kai dalar Amurka 4,290, kimanin Naira Miliyan 1,565,850 a kudin Najeriya.

Jaridar Dabo FM ce ta bankado wannan bayani, inda ta bayyana cewa ta binciko kamfanin dake dinkin irin wannan riguna yana zama a kasar Indiya ne.

KU KARANTA: Shehu Sani: Sai da 'Yar Adua ya bawa Abiola shawara akan ya dauki Atiku a matsayin mataimakinsa yaki yarda

Rigar wacce ke da suna 'Maple Leaf Embroided Silk-Crepe Cape-Back Caftan', ana sayar da ita a shaguna na yanar gizo, irinsu Oscardelarenta da sauran manyan shaguna na saye da sayarwa na kaya masu tsada a yanar gizo.

Sanya rigar da matar shugaban kasar ta yi ya jawo kace-nace sosai a shafukan sada zumunta irinsu Facebook, Twitter, Instagram da sauran su.

Sai dai kuma har yanzu babu wanda ya fito ya kare matar shugaban kasar akan hasashen da jama'a ke yi a kan rigar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel