Ana tare: Shehi Dahiru Usman Bauchi ya goga gemu da gemu da Sarkin Kano (Hotuna)
Fitaccen Malamin addinin Islama kuma jagoran darikar Tijjaniyyah, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kai ziyarar goyon baya da sada zumunci ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a fadarsa dake garin Kano.
Legit.ng ta ruwaito Shehin Malamin ya kai wannan ziyara zuwa fadar Sarkin ne a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni jim kadan bayan saukarsa daga jirgi a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano bayan kammala aikin Umarah.
KU KARANTA: Da arziki a gidan wasu: Mata 2000 daga jahar Adamawa sun ci albarkacin Aisha Buhari
Kai tsaye Shehin Malamin ya garzaya fadar mai marataba Sarki inda suka zauna akan kujera daya suka yi musabaha da juna, sa’annan suka tattauna akan batutuwan masu muhimmanci a tsakaninsu.
A kwanakin baya ne aka jiyo muryar Dahiru Bauchi yana sukar manufar gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na rarraba masarautar Kano zuwa gida biyar.
Dahiru Bauchi yace duk sharrin turawan mulkin mallaka basu taba masarautar Kano ba, don haka bai ga wani kwakkwaran dalili da zai sa Ganduje ya keta mutuncin masarautar ba don biyan wata bukatarsa ba.
A wani labarin kuma tsuguni bata kare ba a rikicin da ake ta kai ruwa ake kai mari tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jahar Kano ba, inda gwamnatin ke tuhumar Sarkin Kano da laifin barnatar da makudan kudade da suka kai naira biliyan 3.4.
Shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado yace babu wanda ke da hurumin hana hukumarsa binciken Sarkin, dama tun a baya ya aika ma wasu manyan hadiman Sarkin da sammaci na su gurfana a gaban hukumar don amsa tambayoyi game da wasu kudade da fadar ta kashe.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng