2019: ‘Dan takarar Jam’iyyar APP ya kai Gwamna Mutawalle kotu

2019: ‘Dan takarar Jam’iyyar APP ya kai Gwamna Mutawalle kotu

Jam’iyyar adawa ta Action Peoples Party (APP) da ‘dan takarar ta na gwamna a zaben jihar Zamfara, Zayyanu Salisu Haske, ta shigar da kara a gaban kotun da ke sauraron karar zaben 2019.

Zayyanu Salisu Haske ya na so kotu ta soke nasarar da Gwamna Bello Mutawalle na jam’iyyar PDP ya samu a zaben da ya gabata. Lauyoyin ‘dan takarar su ka fadawa kotun da ke Gusau wannan.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Laraba, 12 ga Watan Yuni, 2019, jam’iyyar hamayyar ta APP ta na so kotu ta tsige sabon Gwamnan na Jihar Zamfara ne a dalilin rashin takardun karatu.

Lauyoyin Zayyanu Salisu Haske su na ikirarin cewa Bello Mutawalle bai mallaki takardun bokon da ake bukata kafin a tsaya takarar gwamna ba. A cewar sa, Mutawalle bai da isassun satifiket.

KU KARANTA: 2019: Giyar mulki ce ta ke dibar ka - Shehu Sani ga El-Rufai

Masu karar sun bayyana cewa satifiket din wani kwas daga makarantar koyon aiki da ke Garin Banza a jihar Sokoto da Bello Mutawalle ya gabatar a matsayin takardunsa ba su gamsar ba.

Lauyoyin jam’iyyar adawar su na ganin wannan takarda da Bello Mutawalle ya bada bai kai matsayin satifiket ko madadinsa ba. Hakan na nufin Mutawalle bai cancanci ya zama gwamna ba.

A dalilin haka ne jam’iyyar APP ta ke so lallai kotu ta bada umarni ga hukumar INEC na kasa sake sabon zabe ganin cewa ‘dan takarar PDP bai cika sharudan tsayawa takarar gwamna a doka ba.

Haka zalika jam’iyyar adawar nan ta APGA ta ce za ta shigar da na ta karar a kotun sauraron karar zabe. Hakan na zuwa ne bayan kotun koli ta rusa kaf kuri’un da APC ta samu a zaben Zamfara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel