Yadda Hadiza Gabon ta dinga sirfawa wani zagi saboda ya kirata da tsohuwa

Yadda Hadiza Gabon ta dinga sirfawa wani zagi saboda ya kirata da tsohuwa

- Sarakan magana suna cewa idan kasan ta fada baka san ta mayarwa ba

- Mun samo labarin yadda fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Hadiza Gabon ta dinga sirfawa wani mutumi zagi saboda ya kira ta da tsohuwa

- Mutane da yawa sun goyi bayan abinda jarumar tayi, inda wasu kuma suke ganin abinda tayi din bai dace ba

Kwanan nan ne dai fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Gabon ta dora wani sabon hotonta da ta dauka akan shafin sada zumunta na Istagram, domin masoyanta da abokan arziki su kalla.

Kwatsam sai aka jiyo wani daga cikin masu binta shafin nata yayi rubutu a kasan hoton nata a turance kamar haka, inda ya ce: "You looked so beautiful but you are old" ma'ana "Kinyi kyau sai dai fa amma kin tsufa."

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 168 ne ke mutuwa a kowacce rana a kasar Yaman

Hakanne ya tunzura fitacciyar jarumar ta maida masa martani a turance kamar haka: "I am your mother's mate!" ma'ana "Ni sa'ar uwarka ce!"

Hakan shine yadda sarakan magana suke cewa idan kasan na fada baka san na mayarwa ba.

Sai dai kuma bayan jarumar ta mayarwa da mutumin martanin, wasu daga cikin masoyanta sun dan yi korafi akan furucin nata, inda suke ganin abinda ta fada din bai kamata ba. Yayin da wasu kuma suke ganin abinda ta yi din yayi daidai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng