Da alamu Boss Mustapha da Abba Kyari su cigaba da rike mukamansu

Da alamu Boss Mustapha da Abba Kyari su cigaba da rike mukamansu

Yayin da ake jira a jiran a ji labarin wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nada a gwamnatinsa a karo na biyu, mun fara jin kishin-kishin din akwai Hadiman da ka iya yin tazarce.

Rahotanni na yawo daga jaridar The Cable cewa akwai yiwuwar shugaban kasa Buhari ya sake nada Mista Boss Mustapha a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya a wani sabon karo na biyu.

Haka zalika, ana tunanin cewa Malam Abba Kyari ne zai cigaba da aiki a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar. Kawo yanzu dai babu wanda shugaba Buhari ya ba wani mukami.

Har yanzu dai ko da ba a sanar ba tukuna, wadannan kusoshi na gwamnatin shugaba Buhari, su na cigaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda su ka saba tun kafin a ruguza gwamnatin baya.

KU KARANTA: Abin da ya sa Buhari yake so ya koma da wasu Ministoci

Ta ko ina dai ana ta faman neman kamun-kafa wajen shugaba Muhammadu Buhari domin a samu shiga a gwamnatin tarayya. Ministocin da su ka sauka da gwamnonin da su ka sha kasa sun ci buri.

Rahotannin sun nuna cewa ana tunanin ba Tunde Fashola, Ministan babban birnin tarayya Abuja, sai dai kuma kayin da Akinwunmi Ambode ya sha a zaben Legas ya sa lissafi ya fara canzawa.

Shi ma Rotimi Amaechi wanda yana cikin manyan Ministocin da su ka shude zai tashi biyu-babu idan shugaba Buhari bai sake nada sa Minista ba, ganin yadda APC ta gaza shiga takara a Ribas.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel