Yansanda sun kama babban barawon shanu, sun kwato dabbobi 30

Yansanda sun kama babban barawon shanu, sun kwato dabbobi 30

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun kama wani kasurgumin barawon shanu daya addabi al’ummar Fulani makiyaya mazauna kauyen Luma dake garin New Bussa cikin karamar hukumar Borgu ta jahar Neja.

Legit.ng ta ruwaito sunan wannan kasurgumin barawo, Umar Bahago, dan shekara 35 daya fito daga kauyen Kubule dake garin Babana cikin karamar hukumar Borgu. Yansanda sun samu nasarar kamashi ne a mabuyarsa bayan samun bayanin sirri game dashi.

KU KARANTA: Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Yansanda sun kama babban barawon shanu, sun kwato dabbobi 30

Bahago
Source: Twitter

Gab da dubunsa zata cika, Umar Bahago ya tatuke wani mutumi mai suna Buba Adamu, inda ya kwashe masa shanunsa guda 30, wanda hakan tasa mahaifin Buba ya garzaya ofishin Yansandan New Bussa ya kai musu kara.

A cikin tattaunawar da yayi da manema labaru a garin Minna, Umar yace son rai da talauci suka tunzurashi cikin wannan mummunan hali, inda yace yana amfani da kudaden dayake samu wajen kulawa da iyalansa da kuma biyan bashi.

“Ni makiyayi ne, kuma yayana 5, amma kuma babu abinda na tara ma kaina, na san bani da ikon daukan kayan da ba nawa ba, ina da-na sanin wannan abin dana aikata, ina fata matata da yayana zasu gafarta min, saboda matata bata san ina satar shanu ba, amma yanzu data sani na san zata kashe aurenta dani.” Inji shi.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da kama Bahago, inda yace ya amsa laifinsa, kuma Yansanda sun kwato shanun guda 30 dukansu har sun mikasu ga mai su, daga karshe yace zasu gurfanar dashi gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel