Zargin ku a kan Buhari ba gaskiya bane - MURIC ta yiwa NCEF raddi

Zargin ku a kan Buhari ba gaskiya bane - MURIC ta yiwa NCEF raddi

Kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya MURIC, ta yiwa kungiyar dattawan Kirista reshen Arewa NCEF raddi kan zargin wata manufa yayin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya halarci taron musulmi na duniya a kasar Saudiya.

Tamkar sauran kasashe 'yan kungiya, shugaban kasa Buhari a ranar Juma'a 31, ga watan Mayun da ya gabata ya halarci taron kungiyar hadin kan musulunci na duniya da aka gudanar a birnin Makkah na kasar Saudiya.

Wannan lamari ya janyo cece-kuce a fadin kasar nan inda kungiyar NCEF tare da wasu manyan kungiyoyi da dama na Kirista ke ci gaba da zargin shugaban kasa Buhari da yunkurin musuluntar da al'ummar Najeriya baki daya.

Kungiyar NCEF a ranar Alhamis ta makon da ya shude ta kai karar shugaba Buhari zuwa ga kungiyar Tarayyar Turai a sanadiyar halartar taron hadin kan musulunci na duniya da zargin cewar wani yunkuri ne na tursasa akidar musulunci a kasar nan.

Kazalika kungiyar NCEF ta zargi shugaban kasa Buhari da cewar ba ya tabuka wani abun kirki wajen shawo kan kalubale na rashin tsaro dake ci gaba da ta'azzara tare da yiwa kasar nan dabaibayi.

KARANTA KUMA: Rashin wutar lantarki ya hana tattalin arzikin Najeriya bunkasa - Dangote

Sai dai kungiyar MURIC cikin wata sanarwa da jagoranta Farfesa Ishaq Akintola ya gabatar a ranar Juma'ar da ta gabata, ya ce zargin da kungiyar NCEF ta shimfida a kan shugaban kasa Buhari ba su da madogara ta gaskiya gami da shaci fadi marasa hujja.

Farfesa Akintola ya kuma hikaito yadda muhimmancin samun hadin kan wasu kasashen duniya ya sanya kasar Najeriya a shekarar 1969 ta shiga cikin kungiyar hadin kan musulmi ta duniya OIC (Organisation of Islamic Conference) a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon duk da kasancewar sa Kirista.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel