Mutanen Abuja sunyi Allah wadai da furucin shugaba Buhari a kansu

Mutanen Abuja sunyi Allah wadai da furucin shugaba Buhari a kansu

- Wasu mazauna babban birnin tarayya sunyi Allah wadai da furucin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya kira su da 'Masharranta'

- Mazaunan Abujan sun bayyana furucin Buharin a matsayin magana marar dadi a garesu

- Mazaunan sun ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi zabe a Abuja ne saboda wasu dalilai na kuskuren da jam'iyyar APC ta yi

Kwanaki kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana mazauna garin Abuja a matsayin masharranta, saboda sun zabi babbar jam'iyyar adawa ta PDP a lokacin zaben da aka gabatar a shekarar 2019, mutanen garin Abujan sun yi Allah wadai da furucin shugaban kasar.

Mutanen Abujan karkashin wata kungiya ta 'yan asalin garin Abuja, mai suna 'Abuja Original Inhabitants Youth Empowerment Organization' (AOIYEO) a turance, a wata sanarwa da shugaban kungiyar, Isaac David ya fitar, ya bayyana cewa basu ji dadin furucin shugaban kasar ba.

Jaridar Aminiya ta bada rahoton cewa David ya ce shugaban kasar ya ce shi ba na kowa bane, "Mu yadda muka sani shine shi namu ne saboda shine shugaban kasar mu."

KU KARANTA: Kaji tsoron Allah kayi adalci a cikin al'umma - Onitiri ya shawarci shugaba Buhari

Ya ce shugaban kasar ya fadi zabe a Abuja ne saboda wasu kurakurai da jam'iyyar APC ta aikata Abuja.

David yace ya tuna a shekarar 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa mazauna Abuja wani alkawari a fadar sarkin Abaji, na cewar zai bai wa daya daga cikinsu ministan Abuja, amma bai cika alkawarin nasa ba.

"A lokacin zabe shugaban kasa ya tafi jihar Katsina yayi zabe, mataimakinsa ya tafi jihar Legas, haka shima ministan Abuja ya tafi jihar Adamawa domin ya kada kuri'arsa, inda suka bar 'yan asalin garin Abuja suyi zaben su da kansu.

"Wannan dalilin ne yasa dole shugaban kasa ya zabi dan asalin Abuja ya bashi mukamin ministan Abuja, wanda yasan mutanen Abuja yake jin maganarsu kamar yadda kowanne gwamna na jihohi 36 na kasar nan suna fitowa daga jihohin ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel