An kai hari wani babban Masallacin Juma'a na kasar Jamus

An kai hari wani babban Masallacin Juma'a na kasar Jamus

- Wasu mutane sun kai hari wani Masallacin Juma'a a kasar Jamus

- Mutanen da har yanzu an kasa gano ko su waye, sun jefa duwatsu cikin Masallacin, inda suka fasa tagunan Masallacin

A wani gari mai suna Dresden dake jihar Saxonya cikin kasar Jamus, wasu mutane da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kai wani mummunan hari cikin wani Masallacin Juma'a na Fatih wanda yake mallakar hukumar hadin kan Musulunci na Diyanet.

Mataimakin shugaban kwamitin kula da Masallacin Juma'ar Huseyin Tashkin shine ya fitar da sanarwar cewa, wasu mutane da har yanzu ba a san ko su waye ba sun jefa manyan duwatsu cikin masallacin tare da fasa gilasan tagunan masallacin guda uku.

An kai hari wani babban Masallacin Juma'a na kasar Jamus

An kai hari wani babban Masallacin Juma'a na kasar Jamus
Source: Facebook

Kakakin hukumar 'yan sandan garin Dresden Marko Leske ya bayyanawa manema labarai na kasar Jamus cewa, rundunar 'yan sandan bangaren yaki da aikata muggan laifuka ta kasar sun fara gudanar da kwakkwaran bincike akan lamarin.

Ya ce lokacin da aka kai harin babu kowa a cikin Masallacin, amma 'yan sanda sun iske manyan duwatsu an jefa cikin masallacin, wanda suka yi sanadiyyar fashewar tagunan Masallacin guda uku.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke mutane 55 da suke da hannu a kisan mutum 1 da raunata 14 a jihar Bauchi

Musulmai dai na ta kara samun barazana a yankin Turai, inda mutane da yawa suke nuna kyamar su akan addinin Musulunci.

Idan ba a manta ba a watannin da suka gabata, wani mutumi ya kai wani mummunan hari wani babban Masallaci a kasar New Zealand, inda ya kashe mutane masu dumbin yawa ciki hadda yara kanana da tsofaffi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel