Yanzu Yanzu: An kama shugaban CAF, Ahmad Ahmad

Yanzu Yanzu: An kama shugaban CAF, Ahmad Ahmad

An kama shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka Caf, Ahmad Ahmad a Paris babban birnin kasar Faransa.

A cewar @jeune_afrique, an kama shugaban na CAF na a ranar Alhamis da safe a wani Otel a Paris inda ya ke zaune domin hallartar taron FIFA.

A halin yanzu ba a san takamamen dalilin da ya sa 'yan sandan su kayi awon gaba da shi ba duk da cewa a baya-bayan nan an yi ta samun wasu matsaloli a hukumar kwallon da ya ke jagoranci.

DUBA WANNAN: Dan Najeriya ya yi rabon kayan tallafi ga al'umma a masallacin Makkah

Wannan matakin da kwamitin ta dauka ba yiwa magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Esperance dadi ba da ma wasu mutane da yawa a nahiyar Afirka ciki har da wasu manyan magoya bayan Ahmad.

A yanzu dai ba bu tabbas idan kama Ahmad da aka yi yana da alaka da wasan Esperance da Wydad sai dai a farkon wannan shekarar wasu tsaffin ma'aikatan CAF sun zargi Ahmad da laifukan cin hanci da laifuka masu alaka da fyade.

Kakakin NFF, Ademola Olajire ya tabbatar da hakan.

Ya ce: "Eh, yana ofishin yaki da rashawa. An ce ana zarginsa da karya ka'idojin kwangilar da CAF tayi da PUMA wadda ta hada da wata kamfani mallakar abokin Ahmad, Tactical Steel domin sayo kayyakin 2018 CHAN."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164