An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin Oyegun da Oshiomhole

An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin Oyegun da Oshiomhole

Wani babban jigo na jam'iyya mai ci ta APC Mista Yekini Nabena, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta shiga tsakanin rikicin Cif John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar da kuma shugaban ta na yanzu, Kwamared Adams Oshiomhole.

Kiran Mista Yekini na zuwa ne a ranar Laraba yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar The Punch a babban birnin kasar nan na tarayya kan takun sakar dake tsakanin Oyegun da kuma Magajin sa Oshiomhole.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, jam'iyya mai mulkin kasar nan ci gaba da fuskantar kalubale biyo bayan faduwar ta a jihar Zamfara da kuma wasu jihohin kasar nan da ta auku a sanadiyar sabawa ka'idoji yayin gudanar da zaben fidda gwanayen takara.

Ko shakka ba bu kawo wa yanzu bayan kammala babban zaben kasa da zartar da hukunce hukunce na kotu, jam'yyar APC ta sha mugunyar a jihohin Imo, Bauchi, Oyo, Adamawa da kuma Zamfara.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta fara shirye shirye akan kasafin kudin 2020

A sakamakon wannan nakasu da jam'iyyar ta fuskanta ya sanya Cif Oyegun da kuma magajin sa Oshiomhole ke ci gaba da zargi da kuma shafa wa juna bakin fyanti kan wanda rikon sa da kujerar jagoranci ta yi sanadiyar aukuwar wannan lamari na koma baya a jam'iyyar.

Bisa ga madogara ta tabbatar da hadin kai ya sanya Mista Yekini wanda ya kasance kakakin jam'iyyar APC ya nemi shugaba Buhari da ya gaggauta shiga tsakanin tsamar dake tsakanin Oshiomhole da kuma Oyegun inda a cewar kada kuma lamarin ya wuce gona da iri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel