Bikin Sallah: Jerin sunayen hakimai 19 da suka bijire wa sabbin masarautun Ganduje

Bikin Sallah: Jerin sunayen hakimai 19 da suka bijire wa sabbin masarautun Ganduje

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soke hawan Nasarawa da aka saba yi duk lokacin bikin karamar sallah bisa umarnin gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Laraba ne gwamna Ganduje ya umarci sarki Sanusi da ya fasa hawan Nasarawa saboda wasu dalilian tsaro.

Jaridar Daily Nigerian ta ce ta samu labarin cewar gwamnatin Kano ta soke hawan ne saboda takun sakar dake tsakanin sarkin Sanusi da gwamna Ganduje.

Duk da kasancewar gwamna Ganduje ya kirkiri sabbin masaurutu hudu tare da nada sarakunansu na yanka, wasu daga cikin hakiman da suka fada karkashin sabbin masarautun sun bijire wa sabbin sarakunan da Ganduje tare da halartar bikin hawan Daushe da aka yi ranar Laraba.

Bikin Sallah: Jerin sunayen hakimai 19 da suka bijire wa sabbin masarautun Ganduje
Dangote da sarki Sanusi
Asali: Facebook

Hakiman da suka bijire wa sabbin sarakunan sun hada da;

1. Dan Isan Kano hakimin Warawa

2. Dokajin Kano hakimin Garko

3. Dan Galadiman Kano hakimin Bebeji

4. Sarkin Shanun Kano, hakimin Rimin Gado

5. Yariman Kano hakimin Takai

6. Barden Kano hakimin Bichi

7. Sarkin Fulanin Ja’idanawa Hakimin Garun

8. Makaman Kano hakimin Wudil

9. Sarkin Dawaki mai Tuta hakimin Gabasawa

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta kwace rijiyoyin man fetur 6

10. Dan Kadai Kano hakimin Tudun Wada

11. Dan Madami hakimin Kiru

12. Dan Amar Din Kano Hakimin Doguwa

13. Madakin Kano hakimin Dawakin Tofa

14. Matawallen Kano

15. Wakilin Dan Iyan Kano

16. Wakilin Barden Kano

17. Wakilin Dan Makwayo

18. Wakilin Sarkin Yaki

19. Magajin Rafin Kano

Gwamnatin Kano ta saka kafar wando daya da masarauta ne bisa zargin cewar sarki Sanusi na goyon bayan dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, a aben da ya gabata.

Domin rage karfin da sarki Sanusi ke da shi, gwamna Ganduje ya kirkiri sabbin masarautu hudu a Kano wadanda suka hada da Bichi, Rano, Gaya da Karaye.

Duk da wata kotu ta yi kokarin dakatar da gwamnan, ya yi burus da umarnin ta ya nada sabbin sarakunan yanka tare ba su sandar iko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel