Mutane 17 sun raunata yayin da mota ta tumurmusa masu Sallar Idi a kasar Indiya

Mutane 17 sun raunata yayin da mota ta tumurmusa masu Sallar Idi a kasar Indiya

Mun samu cewa kimanin mutane 17 sun raunata yayin da wata mota da ta sharo hanya a guje ta tayi tsani da su suna tsaka da gudanar da sallar Idi a ranar Laraba kamar yadda hukumar 'yan sanda ta bayyana.

Wannan mummunan tsautsayi ya auku a wani babban masallaci dake Gabashin birnin Delhi na kasar Indiya a safiyar yau ta Laraba, 5 ga watan Yunin 2019. Lamarin ya janyo barkewar zanga zanga cikin gaggawa.

A yayin da tuni direban motar ya shiga hannun jami'an tsaro, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kurkusa kamar yadda mataimakin kwamshinan 'yan sanda Meghna Yadav ya bayyana.

An fara gudanar da bincike dangane da yadda rikon sakainar kashi daga bangaren 'yan sa kai da kuma hukumomin tsaro suka gaza bai wa masallata kariya musamman a wannan babban lokaci na Sallar Idi.

KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai za ta gudanar da zaman ta na bankwana a ranar Alhamis

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wani mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutane biyu tare da jikkatar mutane takwas a ranar bikin karamar Sallah cikin birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel