Sarkin Kano ya musanta zargin almubazzarantar da naira biliyan 3.4

Sarkin Kano ya musanta zargin almubazzarantar da naira biliyan 3.4

Fadar mai martaba sarkin Kano ta musanta zargin da hukumar yaki da rashawa da sauraron koke koken jama’a ta jahar Kano keyi mata tare da mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II na yin bindiga tare da almubazzarantar da naira biliyan 3.4.

Legit.ng ta ruwaito walin Kano, Alhaji Mahe Bashir ne ya bada wannan kariya ga masarautar a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, inda yace zarge zargen da ake yi ma masarautar basu da tushe balle makama, sa’annan ya bayyana daki daki yadda masarautar ta kashe kudadenta kamar haka;

KU KARANTA: Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Sabon Sarki bai gaji naira biliyan hudu daga asusun masarautar Kano ba, inda yace gaskiyar abinda Sarki Muhammadu Sunusi II na gada shine naira biliyan daya da dubu dari takwas da casa'in da uku da dubu dari uku da saba'in da takwas da naira dari tara da ashirin da bakwai da kobo talatin da takwas. (N1,893,378,927.38).

Walin Kano yace masarautar ta biya yayan marigayi Sarki Ado fiye da kudi naira miliyan dari a matsayin kudin fansar wasu motocin alfarma da fadar ke amfani dasu, saboda a cewarsu ba motocin masarauta bane, kyauta aka baiwa mahaifinsu.

Haka zalika sakamakon harin da aka kai ma tsohon Sarki, masarautar ta sayo motocin sulke guda biyu akan kudi naira miliyan 142.8, tare da amincewar gwamnatin jahar Kano duba da takardar gwamnati mai lamba SSG/S/D/A/26/T1/109 of 17th September 2014.

Sai wasu motocin alfarma kirar Rolls Royce guda biyu, MS 1 da MS 2 da ake zargin masarautar da saya, inda yace wasu abokanan Sarki ne suka saya masa kyauta, bugu da kari masarautar ta biya N152, 627, 723 ga kamfanin Dobo Gate don mayar da kujeru, gadaje da fankokin gidan sarautar da aka kwashe bayan rasuwar Sarki Ado.

Sanarwar ta kara da cewa masarautar ta kara ma hakimai da dagatai karin albashi, wanda hakan hakan ya daga kasafin albashin masarautar na wata wata zuwa naira miliyan 36, kuma shima wannan ya samu amincewar gwamnati duba da takarda mai lamba KEC/CF/FIN/1/96 of 15th September 2014, kamar yadda batun gyaran gidan Sarki na fadar Kano, Nassarawa da Dorayi ya samu amincewar fadar gwamnati.

Sai dai masarautar tace sau biyu kadai ta taba daukan hayan shatar jirgin sama, na farko lokacin da Sarkin Sunusi II tare da hakimansa suka tafi fadar mai alfarma Sarkin Musulmi don yi masa mubaya’a, sai kuma lokacin da marigayi Galadiman Kano ya wakilci masarautar Kano a wani taro a Nijar.

Bugu da kari masarautar ta biya naira miliyan 154 na motocin tsohon Sarki da aka kai masa hari a cikinsu, sai kuma batun kudaden Data dana kiraye kirayen waya wanda fadar tace an hada na shekaru uku ne, sakamakon Sarki na amfani da layin waya guda daya ne tal.

Daga karshe walin Kano yace a shirye suke su bayar da karin bayani idan bukatar haka ta taso.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel