Mazan Kirista su auri mata sama da guda daya, babu ayar Injila da ya haramta hakan - Fasto

Mazan Kirista su auri mata sama da guda daya, babu ayar Injila da ya haramta hakan - Fasto

- Wani malamin addinin kirista, Rev Vincent Mulwa, ya kalubalanci koyarwar addinin kirista da ke cewa maza su auri mata daya

- Mulwa yace yan Afurka sun fake da koyarwar Turawan mulkin mallaka wadanda suka shigo da addinin kirista Afurka sannan kuma suka yi watsi da auren mata sama da guda daya

- Faston yace babu wata aya a littafin Injila dake goyan bayan hakan

Wani sanannen ilimin addini kuma Shugaban cibiyar Christ Pilgrim Restoration Centre, Kenya, Rev Vincent Mulwa, ya kalubalanci koyarwar addinin kirista da ke cewa maza su auri mata daya.

A wata hira da manema labarai, Rev. Mulwa yace yan Afurka sun fake da koyarwar Turawan mulkin mallaka wadanda suka shigo da addinin kirista Afurka sannan kuma suka yi watsi da auren mata sama da guda daya, al’adan mutanen da suka yi rayuwa a lokutan farko da aka gabatar da littafi mai tsarki.

Rev Mulwa yace yana son shuwagabannin kirista su sake duba akan koyarwa game da auren mace daya, cewa babu wata aya a littafin Injila dake goyan bayan hakan.

Yace wannan ya zama dole a “ceci al’umma mata wadanda ke tsufa a coci ba tare da mazaje ba”.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Kano Sanusi ya yanto fursunoni da naira miliyan 5

A wani labarin kuma mun ji a baya cewa Tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu ta yi tsokaci akan halin da mata kan shiga idan aka ce suna zawarci.

Hafsat wacce ta kasance mata ga marigayi jarumin Kannywood Ahmed S Nuhu ta bayyana cewa zawarci bala’i da musifa ce domin a cewarta da zaran an kira mace da Bazawara toh shakka babu darajarta da kimarta na raguwa a idanun mutane.

Jarumar tace ya kai har idan aka ce mace bazawara ce sai ka ga kowa yana kaffa-kaffa da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel