Jahohin Najeriya 36 da adadin makudan basussukan dake kan kowannensu
Wata jarida dake bin diddigin tattalin arziki, The Economic Confidentila ta sanar da cewa jahar Legas ce kan gaba wajen cin bashi a tsakanin jahohin Najeriya gaba daya, inda take da bashin naira triliyan 1.043 akanta daga ciki da wajen Najeriya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito jahar Legas kadai tana da kashi 20 na jimillan bashin da jahohin Najeriya talatin da shida har ma da babban birnin tarayya Abuja ta ci, inda jimillan bashin ya tashi akan naira tiriliyan 5.376.
KU KARANTA: Daga zuwa biyan kudin fansa, yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin gwamnan Katsina
Sauran jahohin dake bin Legas a wajen cin bashin kasashen waje sune; Edo – naira biliyan 99.45, Kaduna – naira biliyan 81.81, Cross Rivers – naira biliyan 67.95 da kuma jahar Bauchi dake da bashin naira biliyan 48.21 a wuyanta.
A bangaren basussukan cikin gida kuwa, jahar Legas ce ta sake cirar tuta, inda ta jagoranci sauran jahohin Najeriya da bashin naira biliyan 530.243, Delta naira biliyan 228.805, Rivers naira biliyan 225.592, Akwa Ibom naira biliyan 198.663 da Cross Rivers naira biliyan 167.955.
Daga yankin Arewa kuwa, jahar Kaduna ce kan gaba wajen cin bashin kudaden kasashen waje daman a cikin gidan, inda take da nauyin naira biliyan 166.448, sai Bauchi naira biliyan 140.582, sai Kano naira biliyan 139.909, Adamawa 124.863, sai Benuwe naira biliyan 111.608.
Jahohin da suka fi karancin bashi daga ciki da wajen kasarnan kuwa sun hada da Yobe dake da bashin naira biliyan 37.667, Jigawa naira biliyan 36.586, Sokoto naira biliyan 52.723, Katsina naira biliyan 53.220 da Neja naira biliyan 63.915.
Ita kuwa babbar birnin tarayya Abuja ana binta bashin naira biliyan 11.465 daga kasashen waje, yayin da masu bada bashin cikin gida suke binta bashin naira biliyan 164.145, wanda hakan ya kawo jimillan bashin da ake binta zuwa naira biliyan 175.710
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng