Buhari ya goyi bayan kudirin OIC a kan tabbatar da samun 'yancin Falasdinawa

Buhari ya goyi bayan kudirin OIC a kan tabbatar da samun 'yancin Falasdinawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga kudirin kungiyar hadin kan kasashen Musulmi (OIC) na tabbatar da 'yancin Falasdinawa.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda yake gabatar da jawabi amadadin shugabannin kasashen Afrika a wurin taron OIC da aka yi a garin Makkah dake kasar Saudiyya.

A cikin jawabinsa, shugaba Buhari ya ce shugabannin kasashen sun hada kai wajen amincewa da kudirin kasashen kungiyar OIC na tabbatar da samun 'yancin Falasdinawa da kawo karshen aiyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsayi.

Kazalika, ya yaba wa kokarin kungiyar wajen magance rigingimun da aka shafe shekara da shekaru ana fama da su a kasashen Syria, Libya da kuma shiga cikin lamarin tsirarun Musulmin yankin Rohingya a kasar Myammar.

Buhari ya goyi bayan kudirin OIC a kan tabbatar da samun 'yancin Falasdinawa

Shugabannin kasashen dake zaman mambobi a kungiyar OIC
Source: Twitter

Wannan shine karo na 14 da kungiyar OIC ta yi taro tun bayan kafuwar ta.

Sarkin kasar Saudiyya, Salman Bin Adul Aziz As-Saud, ya jagoranci taron a daidai lokacin da wa'adin mulkinsa ya kare. Shugaban kasar Turkiyya, Recep Rrdogan, ya zama sabon shugaban kungiyar OIC.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan kammala taron kungiyar hadin kan kasashen Muslmi (OIC) karo na 14 da aka yi a kasar Saudiyya.

DUBA WANNAN: Gidauniyar marigayi Sheikh Gumi ta karrama Kwankwaso

Da yake sanar da dawowar shugaba Buhari a shafinsa na Tuwita, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya bayyana cewar Buhari ya nuna jin dadinsa bisa yadda kasashen kungiyar OIC suka nuna niyyar bayar da tallafi ga aikin farfado tafkin tekun Chadi.

Tuni sanarwa ta fita cewar shugaba Buhari zai karbi bakuncin shugabannin kasashen gefen tekun Chadi kwanaki kadan bayan dawowarsa daga kasar Saudiyya. Ana tunanin taron ba zai rasa nabasa da gudunmawar da kungiyar kasashen OIC zata bayar ba wajen farfado da tekun Chadi.

A kwanakin baya ne babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antoni Guterres, ya nada shugaba Buhari a matsayin wanda zai zama shugaba na biyu a kwamitin neman hada kudaden da za ai amfani da su domin farfado da tekun Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel